Tsutsar Nama Book 1 Complete Novel Download Pdf

Tsutsar Nama Book 1 Complete By Billyn Abdull

Description/Story:

Tsutsar Nama Book 1! Complete Hausa Novel Document Written By Billyn Abdull

 

Description

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑃𝑎𝑔𝑒 𝑜𝑛𝑒_
_Free page_

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._

………Humm wato Bilyn Abdull atawa fahimtar da abinda shekaran jiyata da jiyata har zuwa yau ɗina tazo min dashi zan iya cewa JARUMTA itace asalin RAYUWA. HAƘURI shike jagorantar numfashi da samun tsahon rai ga kowanne halitta a cikin salama. A duk sanda wasunmu suka tambayemu minene adonmu? Amsa ɗaya muke fara kallo a zukatanmu da furuci (TARBIYYA). Sai dai a gareni ni nace sam ba haka bane. Zan kuma iya faɗa a hankali ko da amsa kuwwa harma da shelantawa. Kada kai mamaki ko fahimtata a bisa tsatstsauran ra’ayina ko zama mai bahagon hasashe. Bance tarbiyya bazata amsa suna ADO ba, sai dai magana ta gaskiya ADDINI shine mafi girman zama ƙololuwar ADO a waje na. Sannan akai kanka da ku kanku duk shine. Ina tsaye bisa wannan ra’ayine saboda ina girmama ADDINI NA bisa koman dake amsa komai na a rayuwa. DUNIYA itace MAKARANTAR farko ga kowanne ma’abocin numfashi, domin a cikinta ake fafutuka da hanƙoron neman SAKAMAKON zuwa MATABBATA. Sobada a yanda ka tafi da ita a haka take baka daraja da kima a wajen komai da kowanka. Kowanne mai numfashi yana tsoron MUTUWA, amma hakan baya hanamu buƙatar RAYUWA da fatan shiga ALJANNA, saboda a canne ake iya samun komai da komai da zukata basa iya hasasowa koda da tsayin motocin hange. Haka zalika ƙarewar kwanakin numfashinmu a kowanne wayewar gari baya hanamu sake tanadin BURIKANMU koda kuwa yaƙininmu na nufin baza muga GOBENMU BA. Duk wani ɗan adam zakiga RAYUWA na taka masa iya rawar abinda littafin ƙaddararsa tazo da shi ne kawai, duk kuma iya hanƙoronka da faɗi tashi akan neman DUNIYA ko guje mata baka isa zartama wannan ƙaddarar taka ba.
Kar na kaiku da nisa bara na baku komai a buɗe a yanda zaku fi fahimtar abinda nake son faɗa ga Bilyn Abdull da ku baki ɗaya. Sunana shine *_SAMRAAH ABDUL-WAHAB GWARZO_*. A zahirin rayuwa ni ɗin ba kowa bace face ɗiyar Malam Abdul-wahab Gwarzo. Domin kuwa mahaifina bai kasance mutum mai mulki ba, haka ba attajiri bane, ba kuma babban malami ba. Shi ɗin driver ne dake aikin tuƙi a wani gidan attajirai. Sai dai ALLAH yay masa rasuwa sakamakon haɗarin mota tun inada shekara bakwai a duniya. Mu uku kacal ya haifa shi da mahaifiyarmu da itama dai ALLAH yay mata rasuwa bayan haihuwar ƙanina tun bamma cika shekara uku a duniya ba. Yaya Musaddiq shine babban yayanmu, sai ni Samraah da autanmu Hafizzullah. Tun bayan rasuwar mahaifiyarmu riƙona ni da Hafizzullah ya koma hannun ƙanen mahaifiyarmu Uncle Imam. Matarsa ita ta ƙarasa shayar da Hafizzullah tare da yaronsu data haifa itama kusan lokaci ɗaya da mamanmu, sai dai bamu da tabbacin ma kota shayar da shi ɗin ko batayi ba. Dan haka suka tashi tamkar tagwaye. Bayan rasuwar mahaifinmu riƙon Yaya Musaddiq ma ya dawo hannun Uncle Imam. Duk da mahaifinmu bamai arziki ko mai mulki bane ya tafi ya barmu da gonakin gado harma da gidan zama. Sai wasu ƴan kuɗaɗe a account. Itama mahaifiyarmu tabar mana gonaki data gada a wajen nata iyayen tare da Uncle Imam dan su biyu kacal iyayensu suka haifa suma. Kasancewar duka iyayenmu a cikin garin Gwarzo suke waɗan nan dukiya tamu duk tana acan ne. Sai gida da muka rayu kawai anan cikin birnin Kano. Karancin shekarunmu yasa duka abinda iyayenmu suka bar mana bayan an raba mana shi ba’a bamu ba, acewar Uncle Imam sai mun girma dan duk shi ya ɗauki komai ya ajiye, gonaki ya cigaba da nomasu, gida ya saka ƴan haya. Uncle Imam shine ya cigaba da ɗaukar nauyin karatunmu dama dukkan al’amura na rayuwarmu har sanda muka kawo girma. Duk da dai rayuwa a gidan Uncle Imam bata taɓa kasancewa mai sauƙi a garemu ba saboda mugun halin matarsa duk mun shanye wannan a ranmu. Amma tabbas mun ɗanɗana kuɗarmu a hannunta akan abubuwa daban-daban. Mun fuskanci ƙalubalen maraici kala daban-daban. Dan komai da zasuyi ma ƴaƴansu yanada bambanci da wanda mu za’a mana. Hatta da abinci takan fifita ƴaƴanta akan mu. Hakama a makaranta suna private school muna government school. Sutura akoda yaushe tasu nada banbanci da namu. Hatta da ɗakin kwana na yaransu nada banbanci da namu. Abin zai baka mamaki idan nace duk wannan wariyar launin fatar muna ganine har daga Uncle Imam bawai ita kawai ba. Kafin mu san kammu mukanyi kuka mu share hawayenmu, bayan mun mallaki hankalinmu musamman ma ni sai na fara maida murtani. Nakan shanye daga ƙyara da hantarar Mom da Abba. Amma bana iya kauda kai daga al’amuran ƴaƴansu. Dan hatta waɗanda suka girmeni idan suka nuna min yatsa saina karya shi nake samun nutsuwa koda za’a rama musu ne. Amma ga Yaya Musaddiq ba haka bane ba, dan shi mutum ne mai shiru-shiru, hakama Hafizzullah baida yawan hayaniya. To nima ɗin dai a zahirance bazakace ina magana ba, dan banda yawan surutu, sannan inada yanayin fuskar salihan mutane. Shiyyasa sometimes nakan aikata abu Mom ta faɗa ace ba’a yarda ba, ni ɗin nan dako yatsa aka saka min a baki bana ciza ba. Wannan halayya tawa na ƙona mata zuciya da ruhi, dan haka nafi sauran ƴan uwana cin wahala da azaba a hannunta harma da hannun Abba ɗin. A haka dai muka rayu cikin haƙuri da juriyar rayuwa har ALLAH yasa muka kammala secondary. Daga nan Abba yace baida kuɗin biya mana mu cigaba da karatun jami’a. Raina ya ɓaci matuƙa domin ganin yanata cuku-cukun biyama Abbas ɗansa dake sa’a da Yaya Musaddiq, da Baby mai sa’a dani. Dan haka na sameshi da batun tunda hakane ya biya mana da gadonmu. A saida gona guda a biya mana. Maruka nasha lafiyayyu masu gigitarwa a wajensa, daga ƙarshe ya koroni da zagi daga falonsa. Duk da ran Yaya Musaddiq ya ɓaci shima baice komai ba, saima faɗa daya shiga min akan abinda nayi. Acewarsa baikamata nayi magana ba, dan koba komai Abba ƙanin mahaifiyarmu ne, ya kumayi wahalar riƙemu kafin yau. Komai bance masa ba, face hawaye kawai da nake zirararwa. Shima bai sake cewa dani komai ba ya fice a gidan.
Kwanaki biyu da faruwar hakan Yaya Musaddiq yazo min da labarin ya samu wajen aikin koyon kanikancin motoci. Duk da ni ba haka nake buƙata ba karatu nake son muyi sai na tayashi murna kawai da fatan alkairi. Daga lokacin Yaya Musaddiq ya fara zuwa gareji, dan koda ya faɗama Abba sai bai wani maida hankali ba face cemasa ALLAH ya bada sa’a a daƙile. Su Baby sun fara zuwa makaranta, yayinda ni kuma na koma mai aikin gidan. Dan dukkan wani aiki na cikin gidan a yanzu ya koma kaina ne gaba ɗaya har wanda banayi a da. Sai idan Hafizzullah ya dawo yake kama min da wasu ayyuka. Ina matuƙar jigatuwa, amma hakan bai hanani shiryawa na tafi islamiyya duk rintsi kuma koda za’a dakeni ne. Tun ma idan na sulale naje na dawo Mom kan dake ni har ta haƙura ta tattarani ta watsar, sai dai dolene bazan fita ba sai na kammala duka aikin data bani, samun wannan damar ya sakani jajircewa na gama komai akan lokaci dan na wuce. A wannan yanayin shekara ɗaya ta shuɗe da kammala sakandare ɗinmu, na samu nasarar yin saukar Alkur’ani, sai dai babu abinda akaimin na walima sai wanda Yaya ya ɗan mun, ban kuma damu ba. Yayinda su Baby keta zuwa makaranta, Yaya Musaddiq na jelen zuwa gareji. Dan in ya fita tun safe sai yamma yake dawowa. Da farko Abba bai damu da aikin Yaya Musaddiq ba balle abinda yake samu, sai daga baya da Mom ta zugashi wai yana samun kuɗi tunda yamun ɗinkin walima sai ya sharɗanta masa yo cefane kullum a gidan. Duk da hakan ya zafi Yaya Musaddiq saboda shi yanada burinsa akan shiga aikin bai nuna ba ko’a fuska, sai ya koma raba kuɗin da yake samu biyu yana ajiye rabi kamar yanda ya saba rabin yana cefanen. A wata ranar da tai dai-dai da cikar shekarar mu ɗaya da watanni biyar da gama sakandire sai ga wani malamin mu yazo neman Abba. Bayan sun ɗan gana na wasu mintuna akai kirana. Ranar da bazan taɓa mantawaba kenan a rayuwata, ranar data zama komai daga cikin TSIRON da yazama shine TUSHEN LABARINA. Ranar da ta zama MAFARIN da har yau ba’a kai ga zuwa ƘARSHE ba tunda numfashi bai rabu da gangar jiki ba…….✍️

 

File Name  Tsutsar Nama… Hausa Novel Doc.
Title   Tsutsar Nama Book 1
Author   Billyn Abdull
Group   Ai  Hausa Novels
Genre   Fiction Story
Published Date   01/01/2024
File Size   500Kb
Format Size   TXT
Phone No  09166221261
Download Tsutsar Nama Book 1 Complete Novel Document By Billyn Abdull

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

Tsutsar Nama Book 1 Complete Novel Download Pdf

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *