💖💖 *MAYRAAH*💖💖
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
Page 24
Washegari da safe Mayraah ta bude idonta a hankali ta dalilin vibration din wayarta, ta mike zaune da sauri ganin gari ya waye kuma ko kiran sallahn asuba bata ji ba, jawo wayar tayi taga Musharraf ne ke kiranta, ta kalli agogon wayar dake nuni da karfe takwas na safe, har kiran ya katse bata daga ba, tayi tagumi tana kallon window din dakin tana jin ciwon cikin har sannan yana damunta sosai, bayan kusan minti sha biyar ta daure ta sauka daga kan gadon a hankali ta nufi bandaki, kafin karfe tara tayi wanka ta shirya, ta dau handout din da take karantawa jiya ta saka a jaka, kallon agogo tayi don makaranta take son tafiya, ta zauna gefen gado tana tunanin ta yanda zata fita ta hado shayi don ta sha magani, ganin lokaci na wucewa ta mike ta nufi kofa ta bude a hankali ta tafi parlor, babu kowa a parlon har ta nufi kitchen sae kuma ta dawo ta tafi window din parlon tana dubawa parking space, juyawa tayi ta karasa kitchen ta hada shayi sannan ta fito, tsaye ta ga Haseenah a parlor don tana jin kamar an bude kofa tayi maza ta fito, duk da yanda gaban Mayraah ya fadi bata nuna hakan a fuskarta ba, don kallo daya tayi mata ta dauke kai tace "Ina kwana" Haseenah dake tsaye sanye da rigan wanda da kadan ya wuce cinya tana kallonta da kyau tace "Ke sae ance kiyi shara da goge goge sannan za ki yi? hankalin ki bai baki abinda ya kamata kiyi first thing in the morning ba kina tashi? ko dai baki ga karfe nawa bane yanzu?" Mayraah na juya shayin hannunta da cokali courteously tace "Yayan bai gaya maki bana shara ba?" Sake baki Haseenah tayi tana kallonta babu ko kiftawa cause she wasn't expecting that, Mayraah ta girgiza kai a hankali tace "Ni ae bana shara...." Tana fadin haka ta juya ta bar ta a wajen ta nufi dakinta ta shiga ta kulle kofa, Haseenah ta kasa rufe baki, she couldn't believe her ears, What??? juyawa tayi ta nufi dakinta kamar zata tashi sama, yanda tayi banging kofar yasa Maheer farkawa ya mike zaune da sauri yana kallon agogo yace "Kin dubo Mimi? Ya jikinta?" Tun dawowarsa sallan Asuba yayi niyyar shiga duba Mayraah, amma Haseenah ta janye hankalinsa tun sannan da bacci ya daukesa sae yanzu ya farka, bai jira Haseenah ta basa amsa ba ya sauko daga kan gadon da sauri ya dau Jallabiyansa zai sa, Haseenah na masa wani kallo tace "Wace Mimin? Yarinyar da ta min rashin kunya yanzu kiris ya rage ta zageni??" Maheer ya juya yana kallonta yace "Rashin kunya kuma?" Kamar zata fashe da kuka tace "Wallahi kuwa dear, daga nace ta taimaka ta ɗan mana gyaran gida ni kuma in nema mana breakfast a kitchen, kawai ta zabga min wata uwar harara wai ance min tana shara ne da zan sa ta shara, ko baka gaya min ita bata shara ba, Maheer i was so shocked, yarinyar nan na fadin haka tayi wucewarta kamar zata bangajeni ta bar ni a tsaye, kai fa kace in zauna lafiya da ita shine har yasa duk na ajiye makaman yaki nace ta taimaka ta mana gyaran gida ni kuma inyi breakfast" Maheer ya karasa saka Jallabiyansa yace "Yeah she is Asthmatic bata shara, sannan bata duk wani aiki da zai yi triggering dinsa, idan me taya ki shara kike so sai a samar maki me aiki karama ta dinga maki" Yana kai wa nan ya fice daga dakin, Haseenah ta bi sa da kallo baki bude, dakin Mayraah ya bude ya shiga ya sameta zaune gefen gado, ya kulle kofar yana kallonta ya nufeta, Kallo daya tayi masa ta ci gaba da shan shayin da ke hannunta, ya karasa ya zauna gefenta yace "Mimi ya jikin? Hope u slept well?" Taki kallonsa tace "Ehh" Shiru yayi, cause kilan yanda ya santa ciki da bai Ammi ma bata santa haka ba, with the way she answered shows that she is angry at him, ya sosa kansa yana kallonta a hankali yace "Ai na shisshigo fa da daddare kina bacci" Ko kallonsa bata yi ba ta ci gaba da shan shayinta, ya ɗan yi shiru, can a hankali yace "Ohk am sorry Mimi..." Ta marairaice tana neman kuka tace "Kasan ai bazan iya bacci ba, kuma shine....." Kawai sai ta fashe da kuka, kame kame ya fara yana bata hakuri, yace "I am so sorry Mimi, i use to over sleep this days saboda aiki yana min yawa, yau ma kawai gani nayi asuba yayi" Ita dai taki cewa komai, yace "Baki ga bread a dinning table ba, bari in je in dauko maki" Yana fadin haka ya mike ya fita, dinning area ya tafi ya dauko mata bread da butter with knife ya dawo dakin, ta ajiye cup din shayin don har ta shanye, yana kallonta yace "Baki son bread din ne kika shanye shayin?" A takaice tace "Eh" Daga haka ta mike ta nufi well ironed hijab dinta ta dauka zata sa, da mamaki yace "Ina zaki?" Ta saka hijab din ta dau handbag dinta tace "School" Yace "Will u be able to cope in school?" Tace "Tunda nayi coping da daddare ai zan iya coping a school ma" Shiru yayi yana sosa keya, can ya kalleta yace "To bari in shirya sai in ajiye ki" Tace "Ina son in hau adaidaita sahu am late already" Yace "I promise i won't waste time" Komawa tayi ta zauna gefen gado ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, yana komawa Bedroom dinsu yaga Haseenah kwance kan gado tana shessheka, har zai shiga bandaki sai kuma ya tsaya yana kallonta yace "Saboda Mimi bata maki shara ba kike kuka?" Mikewa zaune tayi a fusace tace "Yarinya tayi min rashin kunya in gaya maka ka maida ni er iska? Maheer dama dawowa da ni kayi don kai da ita ku dinga walakanta ni a gidan nan? Kanwata ta kusan ta hudu ta min rashin kunya daga dai maganar fatan baki amma ka maida ni er iska?" Maheer na girgiza kai yace "Haseenah karya kike, rashin kunya is the last thing da Mayraah zata maki, i know her too well, ke dai ki nemi wani sharrin da zaki mata amma ba wannan ba, nasan politely zata gaya maki bata shara not rudely, i know Mimi" Yana fadin haka ya shige bathroom ya kulle kofa, wani murmushi Haseenah tayi tana girgiza kafa tana jin zuciyarta na tafarfasa, can tayi kwafa a hankali mike ta fita ta koma parlor, saboda Mayraah Maheer bai bata lokaci wajen shiryawa ba, ya fito ya shigo parlor, kallo daya yayi ma Haseenah ya nufi kitchen, tashi tayi ta bi sa, taga yana zuba ruwan zafi a cup, tayi kasa da murya tace "Baby aiki zaka tafi?" Yace "Ai na ce maki yau zan yi resuming" Sosai farin ciki ya cikata jin zai tafi aiki yau, amma sai ta ɗan hade rai tace "Ko sati daya baza su iya baka ba don Allah, daga aure kwana hudu sai ace ka koma aiki, a ina ake haka, why not ka dau leave kawai ko na sati biyu ne" Shi dai bai ce mata komai ba ya ci gaba da hada shayinsa, Ta marairaice tace "Gashi ban maka komai na breakfast ba, wallahi jiya na zata u were just pulling my legs da kace zaka aiki" Yace "No offense, gobe sai kiyi" Tana murmushi ta rungumosa ta baya tace "To Allah ya kai mu Babyna, amma ka gaya min what will i be cooking for dinner?" Yace "Cook anything" Ta kwanta a bayansa tace "Alright dear" Juyowa yayi suka fita kitchen din tare, a parlor ya zauna yana shan shayin, ita dai tana zaune gefensa yace "Dauko min makullin motata" Mikewa tayi ta nufi dakinsu, tana shiga kiran Badiyya na katsewa a wayarta, ta juya ta kalli kofan da ta rufe kafin ta daga da sauri, Haseenah tace "Yanzun nan ma shirin fita aiki yake, in the next 15 to 20 minutes kawai ki fito" Suna gama magana ta ajiye wayar tana murmushi, sannan ta dau makullin Motarsa da tsadadden turarensa da agogo dake gaban madubi ta fito zuwa parlor, ya mike ya amshi makullin ta fara fesa masa turaren tana cewa "You look cute sweetheart" Ya amshi agogon hannunta yana kokarin saka wa yace "Thank you" Shafa beard dinsa tayi ta marairaice tace "Don Allah Baby ka rufa min asiri kar ka kalli ko wace ya mace idan ka fita, sannan banda sakar ma patient mata fuska har ma da nurses plsss" Murmushi yayi da ya kara fito mata da ainahin kyansa, Haseenah ta kasa daina kallonsa, ya karasa saka agogonsa yace "Baki da matsala" Daga haka ya juya ta bi sa da kallo tana jin wani sabon sonsa, dakin Mayraah ta ga ya nufa, nan da nan ta hade rai har ta daina hangosa, Maheer na shiga dakin ya ganta durkushe bakin gado, ta juya jin an bude kofar dakin, ya karaso da sauri yace "Cikin ne?" Kai ta gyada masa da kyar, yace "You see, i know u can't cope in school Mimi, kiyi hakuri ki bari kawai zuwa gobe in kin kara samun sauki ki je" Cike da karfin hali ta mike tana girgiza masa kai tace "Aa ni zan iya" Da mamaki yace "Like this??" Jakarta ta dauka da wayar ta nufi kofa tana tafiya a hankali tace "Na ce maka zan iya" ya bi ta da kallo har ta fita sannan ya bi bayanta, suna fitowa parlor Haseenah dake tsaye har sannan tana jiran fitowar Maheer ta buda ido da mamaki ganin Mayraah cikin shiri, Maheer yace "Zan ajiyeta makaranta in tafi aiki" Da sauri Haseenah tace "Makaranta kuma Dear? Ba naji kace bata da lafiya ba? Maimakon ta zauna ta huta, me zata je yi a makaranta ita da ba lafiya ba" yace "Ta samu sauki ae" Haseenah taji kamar ta rusa ihu ta ma rasa abinda zata ce masa, Ita dai Mayraah ta karaso cikin parlon tana kallonta tace "Sai anjima" Daga haka ta nufi kofa, Haseenah ta bi ta da kallo, Maheer yace "Sai na dawo" Kin ce masa komai tayi tsabar bacin rai, shi dai ya nufi kofa ya fita, fuuuu ta juya ta koma dakinta. A hanya Maheer na driving wayar Mayraah dake kafarta ya fara vibrate, ya juya yana kallon screen din wayar, tayi silencing kiran bata daga ba, bayan tafiyar kusan minti goma Maheer yace "You are going to school because of him right?" Ta ɗan kallesa da mamaki tace "Why because of him?" Maheer yayi shiru yana ci gaba da driving dinsa, can yace "Toh mu tafi asibiti mana, don nasan ko kinje school babu abinda zaki yi sai kwanciya, i know how u behave during this period of the month...." Mayraah tace "Makaranta zan je i can cope" Bai sake ce mata komai ba har suka isa makarantar, yana isa gaban department yayi scanning parking area din da ido har ya hango motar Musharraf, kashe motarsa yayi ya jinginar da kansa da kujera, Mayraah ta juya tana kallonsa ganin bai bude motar ba, can dai da taga ba shi da alamar budewa tace "Yaya i am late fa" Tada motar yayi without looking at her ya fara reverse yace "Baza ki shiga school din nan yau ba Mimi, when I know babu wani lectures da zaki iya zama a class kiyi attending" Ta marairaice tace "No plss yaya, nace maka fa zan iya wllh" Bai saurareta ba ya ja motar suka bar department din, nan da nan hawaye ya cika idonta ta dinga kallonsa, shi dai bai kalleta ba har suka fita daga school din, ya dau hanyar asibitin da yake aiki..... Har suka isa asibitin Mayraah share hawayen da ya ki tsaya mata take, kiris ya rage ta fashe da kuka, bayan yayi parking ba tare da ya kalleta ba yace "Wajen Dr Musharraf za ki je ba lectures ba, if i may ask, do u still have any business with him?" Bai jira me zata ce ba ya sauka daga motar, ta fashe da kuka sosai, ya zagayo ya bude mata motar yace "Sauko" Ta hade rai ta sauko ya kulle motarsa, yace "Mu je" Tafiya ta fara yi yana biye da ita suka shiga cikin asibitin, gaba daya nurses din sun santa don banda yanzu da karatu yayi mata zafi a da asibitin is like her second home barin idan yana da aiki weekends, to a nan take spending weekend dinta ita ma, tayi composing kanta suka gaisa da nurses din gaba daya ta bar sa reception tsaye ta nufi office dinsa... Tana tsaye ya karaso ya bude office din ta shiga ciki ba tare da ta kallesa ba ta tafi inda take kwanciya duk sanda ta zo, hawaye kawai take a inda take kwance ga ciwon ciki da ya takurata sae juye juye take, kiran Musharraf ya shigo wayarta for the second time tun shigowarsu asibitin, ta mike zaune a hankali tana kallon screen din wayar, leka office din Maheer tayi da yake anyi demarcating inda take kwance da main office din, ta gansa zaune office chair dinsa yana attending to a lady with her baby, Daga kiran Dr Musharraf tayi ta kai kunne tayi shiru, Daga daya bangaren yace "Mayraah" Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace "Ya Maheer yace bazan je school din ba kuma" Shiru Musharraf yayi, bayan few seconds a hankali yace "Ohk" Shiru suka yi gaba daya, can Musharraf yace "Hope you are feeling much better now?" Ta gyada masa kai tace "Alhamdulillah" Yace "Allah ya kara lafiya, sai anjima" Nan da nan jikinta yayi sanyi wasu hawayen suka cika idonta, ta ji ya katse wayar, leka office din Maheer tayi ta gansa shi kadai yana rubuce rubuce, ta zabga masa wani harara kamar yana ganinta, dai dai nan ta ga ya mike ya nufo inda take, da sauri ta goge idonta ta koma ta kwanta ta juya baya ta rufe ido, yana isa wajen ya leka fuskarta yace "Mimi" taki bude idonta, yace "Ina jin ki fa kina waya not long ago" Mayraah tayi still jin abinda yace, sai a sannan ta tuna how sharp his hearing is, ta mike zaune fuskarta babu walwala, yace "Cikin na ciwo har yanzu?" Ta gyada masa kai kawai, yace "In maki allura?" Ta kallesa suka hada ido, shi ya fara dauke idonsa ya juya, sai kuma yace "Bari in kira Amina ta maki" Daga haka ya nufi kofa ya fita daga office din, sae da ya sa ta ɗan ci abincin da aka siyo mata sannan Nurse Amina ta mata alluran, ko minti ashirin ba ayi da mata alluran ba bacci ya dauketa, don dama ana mata alluran take ji kamar an zare mata ciwon... Tun da Maheer ya fita tare da Mayraah Haseenah ta rasa sukuni, tasan zuwa yanzu dai Badiyyah ta kamo hanya, kuma tana zuwa gidan nan tunda har Mayraah bata nan dole hankalinta zai koma kan zancen gold, gaba daya ta rasa yanda zata yi, daga karshe dai ta saka Hijab dinta ta fita compound da sauri, gun mai gadi ta nufa yana gaisheta ko amsawa bata yi ba tace "Malam ya sunanka?" Da ladabi yace "Musa Hajiya" Haseenah tace "Ohk, akwai wata mata da zata zo gidan nan at anytime, zaka ganta doguwa tana da haske, sannan bata kai ni jiki ba, to tana zuwa kace mata babu kowa a gidan kai kadai ne" Mai gadin yace "An gama Hajiya, in sha Allahu" Haseenah ta juya ta koma ciki, wayarta ta dauka ta rufe layin da Badiyya ta san ta da shi yanda tana kira zata ji switch off, sannan tayi dialing number kawarta kuma aminiyarta Salima, Salima na dagawa Haseenah ta saka wani uban shewa tace "Kawata ayyuka sun yi kyau fa ta ko ina in gaya maki" Salima tace "Kai haba, bani labari in sha" Haseenah ta gyara kwanciyarta tana murmushi tace "Wallahi in gaya maki ya dawo yanda kika san wani bita zai zai, kin ma san nawa ya tura min a account jiya da nace masa bani da kudi? Wallahi tunda nake da shi bai taɓa tura min irin kudin ba" Salima ta saki guda tace "To maza a ciko min kudaden mutane in kai masu" Haseenah tace "Kai wannan ai dole ne, don Allah wacece wannan me siyar da kayan nan??" Salima ta kwashe da dariya tace "Aa wallahi bazan fada ba, kinsan babu boye boye tsakanina da ke to nima wllh sarowa nake wajenta in ɗan yi mix sannan in daura nawa riban in siyar, yanzu in na gaya maki ai gun ta zaki nufa direct gashi nata shine sadidan haka kawai ki saka bawan Allah ya zama makale mata ki ja a koresa aiki, gwara dai ki tsaya iya nawa me mix" Haseenah tace "Kai kawata, wallahi ni ko biyanki kika ce inyi sai in biyaki ki bani numberta, fadi price in tura maki yanzu" Salima ta kwashe da dariya tace "Yanzu duk ba wannan ba, Hajiya cikon kudin Malam fa? Kinsan fa har da nasa aikin, ko kinji ya sake maki wancan maganar me muni?" Haseenah tace "Cewa ma yayi sharrin shaidan ne wllh, kar fa ki ji komai duk zan tura kudin casss, sannan akwai ma wani matsalar yanzu haka Salima, amma kinsan ance the wall have ears, don haka mu yi chatting kawai" Salima tace "Toh shkkn bari in kunna data" Katse wayar Haseenah tayi ta bude WhatsApp dinta. After sleeping all day Mayraah ta bude idonta a hankali ta dalilin hannun da taji a forehead din ta, suna hada ido ta mike zaune da sauri tana murza ido tana kallonsa, yace "How are you feeling?" A hankali tace "Alhamdulillah, ina yini?" Yace "Lafiya lau" Maheer ya karaso wajen nasu yana kallonta yace "Are you okay now?" Ta gyada masa kai, Usman ya juya ya koma kan kujera ya zauna, Maheer yace "Me za ki ci?" Usman yace "I will get her, idan mun fita, it's getting late now" Maheer yace "Ohk, baza ki shiga bandaki ba, za ku fita da Barrister" Mayraah ta kalli Usman, sai kuma ta sauko daga kan gadon ta dau handbag dinta ta nufi bandaki, zata iya daukan pad a gaban Maheer but not Usman tun tasowarta, Maheer dai ya bi ta da kallo ya koma office chair dinsa ya zauna, ko da ta fito daga bandaki Maheer kawai ne a office din, yana kallonta yace "Yana jiranki a mota" Ta marairaice tace "Ina za mu je yaya? Kasan bani da lafiya" Maheer yace "Ai ba dadewa za ku yi ba, zai dawo da ke soon" Ta ɗan yi shiru, sai kuma ta nufi kofa ta fita......
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence 07087865788
Mayraah Page 25 By Khalesat Haiydar
0 Comments