💖💖 *MAYRAAH*💖💖
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
Page 23
Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga our very own Barrister Inna (Aunty Fatima) Allah Ubangiji ya iya maki, ya raya maki zuri'a, ya kawo cinikin turaren wuta kaca kaca ki bude plaza a Gombe kina daddaga shoulders🥰
Lush and Scrumptious (The Mardiyya without letter R) da kawarta ICE, kuma na gaisheku da fatan alkhairi Allah ya kawo maku mazaje na gari, Sis Aisha Abba (Ummu Janan) i greet you and Baby Janan, Allah ya raya maki ita yayi mata albarka🥰
My lovely fans, i love u all as always, Allah ya iya maku💖
Mayraah na zaune kan darduma tun bayan da ta idar da sallahn isha bata tashi wajen ba tayi nisa tunanin da take ta ji an bude kofar dakin, da sauri ta juya tana kallon kofar, Maheer ya shigo da sallama rike da plate da ledan takeaway din abinci a hannunsa, karasawa yayi kusa da ita ya durkusa ya ajiye ledan ya ciro takeaway din ciki sannan ya juye a plate, ya daga kai suka hada ido ya sakar mata murmushi yace "Ur favorite" Ta sauke idonta tace "Thank you" Yace "Kinyi wankan?" Ta gyada masa kai, ya mike yace "Ohk bari in saka maki kayanki a press kafin ki gama cin abincin" Yana fadin haka ya mike ya nufi akwatunanta guda uku dake dakin ya bude guda daya, ta maida dubanta kan abincin gabanta ta fara ci a hankali, Absentmindedly take cin abincin da ko taste dinsa bata ji a bakinta, bayan wani lokaci ta juya taga ya bude wani akwatin with her inners inside, da sauri ta ajiye spoon din hannunta tace "Aa, ka bar min wannan zan yi da kaina" Ya juya ya kalleta yace "Ohk" maida akwatin yayi ya bude wani, ta ci gaba da cin abincinta, har ya gama jera mata duk kayan a press ko quarter din shinkafar bata iya ta ci ba, ya dawo kusa da ita yace "You are not eating Mimi, ko baki son shinkafan ne yau?" A hankali ta matsar da plate din tace "Na koshi" Yace "Ko in kawo maki Milo?" Ta girgiza masa kai tace "I am full" ya dau ledan maganin da Dr Musharraf ya siya mata ya fiddo su yana duba su, ita dai kallonsa kawai take, after examining the drugs ya ballar mata su ya mika mata yace "Take" ta mika hannu ta amsa sannan ta sha da ruwan goran dake gefenta, yace "Tunda baza ki ci abincin ba ni bani in ci" Daukan plate din tayi ta mika masa ya amsa, ta mike ta shiga bandaki zata wanke bakinta, Maheer ya juya yana kallon gefensa, Hijab dinta ya tsura ma ido for few seconds, can ya dauka ya kai hanci yana perceiving din scent din Hijab din, dai dai nan ta fito tana cewa "Yaya babu toothpaste a ciki" Shiru tayi tana kallonsa, ya ajiye hijab din da sauru yace "Oh ok bari in dauko maki yanzu" Yana fadin haka ya ajiye plate din hannunsa ya mike ya fita daga dakin, Mayraah ta karasa bakin gadon ta dau Hijab din nata ta kai hanci ita ma, ajiyewa tayi ta sauke idonta kasa ta juya a hankali ta koma inda take tsaye, can kuma ta sake komawa gun Hijab din ta dauka ta shiga bandaki ta saka a bucket ta zazzaga detergent dake cikin bandakin ta bude pampo, yana dawowa dakin ya kwankwasa mata bathroom din, ta bude kofar ta amshi toothpaste din sannan ta kulle, juyawa yayi ya dau abincin da ta bari ya fita daga dakin, Mayraah ta gama wanke bakinta ta dauro alwala ta fito, kwanciya tayi gefen gadon ta lumshe ido after so many thought that ran through her mind bacci ya dauketa, Wajen karfe goma Maheer ya shigo dakin, ya karaso kan gadon yana kallonta yace "Kinyi alwala kafin ki kwanta Mimi?" Kai kawai ta gyada masa idonta a lumshe, yace "To gyara kwanciyarki" Ta koma middle of d bed ta kwanta, ya rufa mata duvet yace "Don't forget to pray" Ta gyada masa kai, ya rage AC, ya kashe wutan dakin gaba daya sannan ya fita ya kullo mata kofar. Washegari da asuba Maheer zai tafi masallaci ya shigo dakin don tada ta, bai yi mamakin ganin ta tashi ba don a gida karfe biyar take tashi dama, ya fita zuwa masallaci, Mayraah na idar da sallah ta koma ta kwanta, for the past 4 days sai jiya tayi bacci sosai da daddare yanzun ma kuma wani baccin take ji kilan har da maganin bacci a magungunan da Musharraf ya bata, karfe takwas da kusan rabi ta farka, da sauri ta mike bayan ta tuna ai zata school yau, ta shiga bandaki don yin wanka, kafin tara da rabi har ta gama shiryawa, ta zauna gefen gado tayi jim tana bin dakin da kallo, babu abinda babu ciki, and it look beautiful, can dai ganin lokaci na wucewa kuma karfe goma take da lectures ta mike ta nufi kofa ta bude a hankali, main parlor ta shigo, ta dinga bin parlon da kallo, sosai parlon ma ya hadu yayi kyau, cream with touch of gold ne yawancin abubuwan parlon, ta kalli hanyar kitchen sannan ta nufi can, tana bude kofar ta gansa tsaye yana peeling Irish, ya juya yana kallonta yace "Good morning Mimi" A hankali tace "Good morning Yaya" Yace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kin yi bacci sosai?" Ta gyada masa kai, yace "That's great" Karasawa tayi cikin kitchen din tace "Kawo in fere" Yace "Aa ke da baki da lafiya, kawai kije kiyi kwanciyarki i will serve u breakfast in bed...." Ɗan murmushi tayi wanda iyakarsa lips dinta tace "Ni dai ka kawo inyi zaka bata min lokaci" Juyawa yayi yana kallonta yace "Yunwa kike ji ne?" Ta girgiza kai tace "Aa, zan je school" Shiru yayi sai kuma yace "No Mimi, ki bari zuwa Wednesday, kin ga u are just recovering, kar ki yi stressing kanki" Tace "Pls ina son inje, I've missed a lot, and our exams is in 4 weeks time" bata jira me zai ce ba ta amshi peeler din a hannunsa ya sake mata ya koma gefe yana kallonta, ta fara fere irish din, juyawa yayi ya fita daga kitchen din, before 10:15 har ta gama ta soya kwai ta dafa ruwan shayi ta fito parlor da fried Irish and egg din, ganin baya parlon ta kai masa dinning ta ajiye sannan ta ja kujera ta zauna tana jiran shayinta ya huce, sai gashi ya shigo parlon, dinning area din ya karasa yana kallon plate din irish dinta wanda bai wuce kwaya biyar ba da karamin kwai a gefe yace "Meye wannan din Mimi?" Ta daga kai tana kallonsa, daukan plate din yayi ya juye abincin nata a nasa sannan ya kai middle of the parlor ya ajiye, ya koma ya dauko shayinta da nasa ya ajiye a parlon ya zauna yana kallonta yace "Dawo nan mu ci" Ta marairaice tana kallonsa, can ta kalli agogo ganin she is wasting her time ta mike ta tafi parlon ta xauna gefensa ta fara cin irish din, haka nan yayi forcing dinta sai da ta ci da ɗan yawa ta sha shayinta, 10:40 ya tafi da ita school din a motarsa.... Gaban department dinsu yayi parking yana kallonta yace "Yaushe za ku gama lectures?" Tace "4pm" yace "Ohk i will be here by 4" Tana kallonsa tace "Aa kawai zan samu me adaidaita sahu Yaya" Yace "Aa for today zan dawo in dauke ki" kudi ya ciro a aljihunsa yace "In case zaki ci abinci a cafeteria" Ta girgiza kai tace "Bazan ci komai ba" Yace "To amshi dai" karban kudin tayi tace "Nagode" Yayi mata sallama ya bar wajen, shiga department din tayi, tasan yanxu duk an shiga lectures, kawai ta tafi inda suke sallah ta zauna, shiru shiru ita dai bata ga shigowar Dr Musharraf ba har kusan 12, lokaci daya mood dinta ya canza gashi bata fito da waya ba balle ta kirasa, sai ga Coursemates dinta sun fara fitowa daga lecture hall, Hamidah na ganinta ta nufota da sauri tace "Lahh Mayraah, ashe kin shigo" Mayraah ta mata murmushi tace "Eh na shigo, Ya lectures din?" Hamida ta zauna gefenta tace "Alhamdulillah, na ma rubuta maki attendance, to me yasa baki shigo hall ba" Mayraah tace "Na ga time ya wuce ne shi yasa" Hamidah ta sauke ajiyar zuciya tace "Bari in nuna maki note din da muka yi, ya su Ammi?" Mayraah ta sauke idonta kasa tace "Suna nan lafiya" Da alama Hamidah bata son kawo ma Mayraah maganan aurenta da aka fasa shi yasa take ta kame kamen nuna mata note, ta ciro notes dinta ta mika ma Mayraah tace "Iyakar abinda muka yi kenan, nasan a yau duk za ki karance" Mayraah tayi murmushi ta amsa tana dubawa, nan sauran Coursemates dinsu suka nufo su ganin Mayraah, duk aka gaggaisa, babu dai wanda ya kawo mata zancen fasa aurenta, har suka shiga second lectures din ranan Mayraah bata da wani walwala balle sukuni, bata taɓa tunanin bazata ga Dr Musharraf a school ba yau, but he told her he will be coming, he didn't keep to his words, a haka dai suka gama lectures din wajen karfe hudu suka fito, sai da suka yi la'asar sannan Mayraah suka fito department din tare da Hamidah, Motar Maheer ta gani a inda ya tsaya da safe, Tana kallon Hamidah tace "Ya Maheer ya zo zai daukeni, mu je sai mu rage maki hanya" Hamida tace "Ai ko nagode" Tare suka tafi gun motar, Mayraah ta bude front seat, Hamidah ta shiga baya, bayan ta zauna ta gaida Maheer, ya amsa da fara'a yace "Ya lectures Hamidah?" Tace "Alhamdulillah" yace "How is preparation for exams?" Tace "Muna ta yi" Yace "To Allah ya baku nasara" Hamidah tace "Ameen mun gode" Mayraah ta kallesa ta gaishesa, ya amsa sannan suka bar gun, dai dai inda Hamidah zata samu adaidaita sahun anguwansu Maheer ya ajiyeta, ya bata 2k kudin ɗan sahu sannan ya kama hanyar gida tare da Mayraah, sai da ya fara tsayawa a hanya yayi masu takeaway din abinci sannan suka karasa gida.... Yana parking a parking space Mayraah ta dau ledan takeaway din ta bude motar ta sauka, shi ma ya sauka, yana kallonta yace "Haseenah is back" Sosai gabanta ya fadi sai dai bata ce komai ba, yace "Mu je mana" Ta fara tafiya ya bi bayanta har suka iso kofar parlon, ta bude kofar ta shiga da sallaman da tayi a ranta, Haseenah na zaune parlorn ta cakare dankwaki a kan doguwar rigar jikinta tana taunar cingam, tun da ta ji shigowar motar Maheer ta fito parlon ta zauna dama, Suna hada ido Mayraah tace "Ina wuni" Haseenah ta kalli Maheer dake bayan Mayraah a takaice tace "Lafiya" Mayraah ta ajiye ledan hannunta ta wuce daki, Maheer ya karasa parlon ya zauna yana kallon Haseenah yace "I dislike this gum u are chewing Haseenah, ke baki gaji da tauna chewing gum making that awful sound?" Mikewa tayi ta bar masa parlon ta yi hanyar dakinta kamar zata tashi sama, ya bi ta da kallo sannan ya mike ya bi bayanta, a daki ya ganta zaune gefen gado ta jefar da dankwalinta, yana kulle dakin ta fashe da matsanancin kuka tace "Maheer tun da nake ban taɓa ganin inda daga tarewar amarya da kwana uku za a kawo mata zankadediyar budurwa haka a ajiye a gida ba, yanzu kai a tunaninka adalci aka min? Wannan wani irin shiga hakki ne? Ko amarci na baza a bari in gama ci lafiya ba, da can kai kake rike da ita ko duk don a musguna min ne yasa za ace zata dawo gidan nan da zama, bikina haka nan aka yi sa a gantale saboda ita, ko daurin auren baka je, babu wani program da aka yi, sai yanzu kuma ka kawo min ita kace nan zata zauna" Tana kai wa nan ta fada kan pillow ta fashe da matsanancin kuka, Maheer yayi shiru yana kallonta, can ya sauke boyayyen ajiyar zuciya ya karasa kusa da ita ya zauna gefenta ya dagota, yayi kasa da murya yace "Kiyi hakuri Haseenah, that wasn't the plan wllh, kuma ban yi hakan don in shiga hakkinki kamar yanda kika ce ba, ban taɓa kawowa a rai Mayraah zata zauna gidana ba, abubuwa ne suka zo da haka, and Mayraah is only staying here for the meantime not forever, kiyi hakuri don Allah ki min alfarma ta zauna gidan nan zuwa wani lokaci, kinga zata taimaka maki wajen aikin gida, and Mayraah bata da matsala komai kika sa ta zata maki, pls albarkacin soyayyan da kike min kiyi hakuri ku zauna lafiya, her staying here is just for a while i promise u" Ita dai goge hawayenta kawai take tana wani cika tana batsewa, ya rungumeta yana shafa gashin kanta yace "Kin ji dear" cike da shagwaba tace "Shi kuma walakanta ni da kayi 3 days ago fa?" Yayi kasa da murya yana kallonta kasa kasa yace "Sharrin shaidan ne dear, i don't know what came over me that day, forgive me pls" Sai dab da magrib Maheer ya fito dakin Haseenah, da mamaki yake kallon ledan abincin da suka siyo daxu dake saman center table, juyawa yayi da sauri ya nufi dakin Mayraah, zaune ya ganta kan darduma da materials din karatu a gabanta, ta daga kai tana kallonsa, da damuwa yace "Dama baki dau abincin ba Mimi?" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, juyawa yayi ya koma parlon ya fara dauko plate a kitchen da goran ruwa a fridge sannan ya dau takeaway din ya nufi dakinta, Haseenah da ta fito parlon sanye da wata er dangalalliyar riga ta daura karamin towel a kanta ta bi sa da wani kallo tana kyabe baki, can ta ja tsaki, Maheer na shiga dakin ya duka gaban Mayraah ya zuba mata abincin, ba tare da ya kalleta ba yace "I am sorry Mimi, i slept off, ban san baki dau abincin ba" ita dai bata ce komai ba, bai bari sun hada ido ba ya mike ya fita daga dakin. Haseenah na zaune parlor tana danna wayarta Maheer ya fito daga Bedroom dinsu bayan yayi alwala, yana kallonta yace "Zan je masallaci, ke baza kiyi sallan bane kike zaune nan?" Ta langwabar da murya cike da shagwaba tace "Zan yi mana, Baby don Allah gasasshiyar kaza nake sha'awar ci" yace "A ina za a samo kaza yanzu?" Ta wani turo baki tace "Ai ka fi ni sani, kawai ka fita da motarka kayi parking a waje, ana idar da sallah ka tafi ka siyo min ni dai" Ya ɗan yi jim sai kuma ya juya ya koma daki ya dauko makullin motarsa sannan ya fita daga parlon, ta tafi window da sauri tana leka compound har ta ga ya fita da motarsa sannan ta dawo parlon, Zaunawa tayi ta dau wayarta ta yi dialing number Badiyya, yana fara ring kamar jira Badiyya take ta daga cikin fada tace "Wai ke Haseenah baki ganin kirana ne? Ban fa gane abinda kike nufi da ni ba ina ta binki ki bani kayana kin ki, kin fa san halina sarai Haseenah, ina ta bin ki a hankali kina raina min wayo ko? nace na fasa siyar da gold din nan ki bani kayana ko ana dole ne?" Haseenah ta katse ta tace "Ke dai baki da hakuri wllh Baddiee, gwal dinki dai na nan ki kwantar da hankalinki, kinsan dae bazan cuce ki ba kawata" Badiyya tace "Haba wannan ai ya fara zama rainin hankali, abu kusan sati daya yanzu kina ta yawo da hankalina, gashi bani da ko sisi a account sai da na siyar da zobuna na biyu na biya bashin da ake bi na sannan na samu kwanciyar hankali, sannan inyi ta kiranki ki ki daga wayata, ni dai yanzu ki gaya min kina ina?" Haseenah tace "Labari na kira in baki da dumi duminsa" Badiyya tace "Haba dai, Maheer din yaje Zarian ne?" Haseenah tace "Wani Zaria? gani nan a gidansa yanzu haka nake gaya maki har abu ma ya sake kankama, ashe dama da gaske kike da kika ce min Hajja taje ta kori Mayraah a can gidan?" Badiyya tace "Au da ke kin zata wasa ne, ae ina nan ina ta zugata duk abinda za ace mata kar ta saurara kowa, har Ammi taki saurara tace sai dai Ammi ta zabi ko ita ko Mayraah, Abba ma dazun nan ya bar parlon nan, kinsan shi ma yana respecting dinta sosai kuma yana jin maganarta, kuma baya son abinda zai daga hankalin Ammi, to duk da zuwan Abba har yanzu Hajja na kan bakanta, yanzu zancen da nake maki ba a san inda Mayraahn ma take ba, wa ya sani ko duniya ta shiga, kinga dama ni da ake ma kallon er duniya ai gwara ita ma ta zama er duniyar, Allah Ubangiji ya sa ta fada hannun uwar karuwai, Magajiya ake ce mata ko me? Ita dai, ko kuma Allah ya sa ta fada hannun ɗan iska yanda cikin kankanin lokaci zai lalatata yayi lagos ko tafa da ita, daga nan kin ga ta samu hanya ai, kawai fatana kenan Allah kada ya bata ikon fadawa hannun kirki, kuma Allah ya kara hankadata tayi gaba yanda ko waiwayo mu bazata sake yi ba, Musharraf kuma dama sai gani sai hange a gareta, tana ji tana gani zan auresa...." Haseenah tayi wani dariya tace "Wani duniya?? To ga Mayraah a gidana" Badiyya sai da ta mike tsaye daga kwancen da take tsabar shock, da wani irin mamaki tace "Gidanki kuma??" Haseenah tace "Wallahi kuwa nake gaya maki Badiyyah" Cike da confusion Badiyya tace "Gidanki fa kika ce Haseenah?" Haseenah tace "Karya zan maki ne? To ta ma rigani dawowa gidan in gaya maki, nima dawowa nayi na samu har ta tare a nan, ga daki an mata furnishing kamar amarya, an zuba mata komai a bathroom, ga kayanta ta jera reras a sipp" Badiyyah tayi mitsi mitsi da ido tace "Kan uban cannn, kuma kika yarda Haseenah???" Haseenah tace "Ohh ashe baki yi trusting dina ba kenan Badiyya, ae a halin da ake ciki yanzu dole in nuna na yarda, sannan in nuna kamar ba komai, dalilin da yasa Maheer ya maido ni cikin sauki kenan fa, ke kin zata haka kawai Maheer zai bi ta kaina kwana kusa? kinga dole nima inyi melo for now, amma hauka ake da Mayraah zata zauna gidana inyi shiru in koma gefe in zuba ido, yarinyar da na tsana tun ma ba a san wacece ita ba balle yanzu da nasan babu hadinta da Maheer na gano mara asali ce ita tsintattciya" Badiyya tace "Tabdijam, wato saboda ya nuna ma Hajja iyakarta shi yasa ya daukota ya maida ta gidansa kenan, ke kuma kika yi shiru kika amince saboda kina son a maido ki" Haseenah tace "Ke wai baki san komai dan siyasa bane Badiyya, yarinyar da duk duniya nake jin bbu warce na tsana irinta ne zan yarda mu zauna lafiya under same roof?? Inaaa ai kema kinsan bazai yiwu ba" Badiyya tace "Ya fara fita aiki ne Maheer din?" Haseenah tace "Naji dai yana cewa gobe zai je aiki" Badiyya ta gyada kai tace "To maa sha Allah, zan kiraki goben" Haseenah tace "To Allah ya kai mu, ai ina ga daga karshe duniyar ma zata gwammace ta shiga da dai ta zauna gidan nan" Badiyya tace "Aa tun yaushe, ke dai kawai mu yi waya gobe" Daga haka ta katse wayar, Haseenah ta dinga girgiza kafa tunanin ta inda zata fara na yawo a brain dinta, can tayi wani murmushi tana kallon hanyar dakin Mayraah tace "Zaki gwammace shiga duniya da zaman gidana" Tana fadin haka ta mike fuuu tayi hanyar Bedroom dinta ta shige ta kulle kofar. Wajen karfe bakwai da rabi Maheer ya shigo parlon, Haseenah na jin shigowar motarsa dama ta fito da sauri, da ido take binsa har ya karaso tsakiyar parlon ya ajiye leda daya, ta dinga kallon ikon Allah taga yanda zai yi da dayan, hanyar dakin Mayraah taga yayi, da hanzari ta sha gabansa tana masa wani kallo tace "Ban gane ba Maheer, ita ta aike ka halan? Meye wannan din zaka kai mata" Maheer ya hade rai yace "Hey Haseenah, do not start this with me, kina ganin zan ci abu ne in hana kanwata a gidan nan? Are you even okay? Kinga in kina so mu zauna lafiya ki cire idonki a duk abinda za ki ga nayi ma Mayraah, ina ta lallaba ki tun dazu kada ki bari inyi displaying my other side" Barin ta yayi wajen a tsaye ta bi sa da kallo baki bude, yana bude kofar dakin Mayraah yaji ta sa makulli, dama tun da taji fitar motarsa ta kulle dakin da makulli, ya kwankwasa kofar yace "Mimi open the door" mikewa Mayraah tayi daga inda take duke tana karatu, tun bayan da ta idar da sallahn magrib taji alamar cikinta zai fara mata ciwo, ta karasa ta bude kofar, mika mata ledan hannunsa yayi yana kallonta yace "Do you need any other thing?" Ta ɗan yi shiru tana kallonsa, sai kuma tace "I need sanitary pad" Yace "Oh.. ok" Juyawa yayi ya bar wajen, Mayraah ta mayar da kofar ta kulle da lock, Haseenah dake tsaye parlor har sannan ta bi Maheer da kallo ganin ya nufi kofa, tana jin sa ya sake fita da mota, ta zauna gefen kujera zuciyarta na tafarfasa tana kokarin calming kanta down, sai kusan 8 Maheer ya dawo gidan, Haseenah na jin shigowarsa gidan tun bai karaso cikin parlor ba ta shige dakinta ta rufe kofa, Maheer yayi knocking dakin Mayraah ta bude, ya mika mata ledan hannunsa yace "Akwai magani a ciki, i don't know ko zai maki naga yanzu baki son allura" Tace "Zai yi, nagode" Yace "Let me get u hot water" Ta gyada masa kai, kitchen ya tafi ya dafa mata ruwan zafin ya zuba a flask ya kawo mata har da cup, ta amsa tana kallonsa tace "Nagode yaya" Yace "Take care of ur self" Ta gyada masa kai, yana barin wajen ta kulle dakinta. Har dare ya tsala Mayraah bata yi wani bacci ba saboda ciwon mara, Maheer na kwance amma gaba daya tunaninsa na kanta cause yasan yanda cramps ke mata, ya kuma san wahalan da take sha, in da gida ne har ayi asuba ya dinga shiga dakinta yana dubata shi da Ammi, but now baya son issue da Haseenah dake gefensa, yana fita dakin nan yasan sai ta bi shi ya zamar masu bacin rai, haka nan ya dinga juye juye all his thinking akan Mayraah, kasa daurewa yayi daga karshe ya mike zaune yana kallon Haseenah dake baccinta hankali kwance, taba ta yayi yace "Dear...." Ta bude ido a hankali, ya kunna closet light din dakin, ta mike zaune tana murza ido tana kallon agogo dake nuni da karfe biyu da rabi tace "Baby lafiya, why are you awake?" Yace "Erm pls, i want you to check on Mayraah bata da lafiya, ni ina fita yanzu zaki iya maida shi issue" Tace "Bata da lafiya? Shi yasa ka kasa bacci? To me ya sameta?" Yace "Ban gane na kasa bacci ba, u have started again ko?" Tace "To nace me ya sameta?" Yace "Ki je ki dubata" Sauka tayi daga kan gadon da shegun kayan baccin jikinta zata fita daga dakin yace "Haka za ki fita?" Juyawa tayi ta kallesa tace "Wajen namiji zan je halan?" Yace "Plss cover ur body before going out Haseenah" ta wani kyabe baki ta dau zani ta daura sannan ta fita dakin.... Mayraah na durkushe a dakin ta daura kanta saman gadon wayarta dake gefenta ya fara vibrate ta jawo wayar da kyar ta daga ta kai kunne amma bata ce komai ba, daga daya bangaren yace "Kin samu kin sha ruwan zafin?" kai kawai ta gyada masa, yace "Har yanzu kuma baccin bai zo maki ba?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "You are not saying anything ko dai baccin kike ji Baby?" Kamar zata yi kuka tace "Aa" a hankali yace "I wish I can take away the pains for you" Ita dai bata ce komai ba don azaba ya isheta, yace "Ko za ki sake shan maganin" da kyar tace "Na sha sau uku ai" shiru yayi yana jin tausayinta har cikin ransa, cike da karfin hali tace "Ina zuwa" Yace "Aman ne dai?" Tace "Eh" Ajiye wayar tayi ta shiga bandaki da sauri, Haseenah ta gama zagayenta a corridor din dakunan bayan yan mintuna ta koma dakinsu tana kallon Maheer dake zaune, ta kashe closet light din dakin tace "Bacci take yi, kai ma sai ka kwanta kayi bacci" Bata jira me xai ce ba ta shige jikinsa.... Har karfe hudu Dr Musharraf bai yi bacci ba kamar yanda Mayraah bata yi ba, every few minutes xai kirata to check on her, har dai ya kirata around 4:45 yaga bata daga ba, nan ya gane bacci ya dauketa....
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Mayraah Page 24 By Khalesat Haiydar
0 Comments