💖💖 *MAYRAAH*💖💖
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
Page 21
Mikewa Usman yayi da sauri yana kallon Abba cike da mamaki, tsabar yanda maganar Abba ya zo masa a ba zata kasa cewa komai yayi, can dai yayi gathering courage yace "In auri Mayraah fa kace Abba? Did you mean it? How? Mayraah da muka taso nake ma kallon kanwata Muharramata how zan aureta as wife? This sounds more like an abomination to my ears, it's weird, ta yaya zan auri kanwata da nake ma kallon uwarmu daya ubanmu daya kawai don abun nan ya faru? No pls tell me ta yaya Abba?" Komawa yayi ya zauna ya ciro handkerchief yana share zufan da ya keto masa a forehead, he looks so confuse, yana girgiza kai yace "No Abba, this isn't going to work, Mayraah kanwata ce har yau, har gobe, har abada, bayan wannan babu wani kallo da zan sake mata, kanwata ce ita ta jini...." Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "It's okay Usman, i understand you, but we all neva bargained for this, kawai abinda yasa na kawo shawaran nan naga abinda muke boyewa for many years an tonosa ta hanyar da bamu taba zato ba bamu yi tsammani ba, sannan duk wanda zai zo neman auren Mayraah ina da tabbacin tun daga waje za a tsegunta masa asalin wacece ita, my wish yanzu a rayuwa bai wuce ace Mayraah ta wuce gori ba, i want her to live like every other person, kuma nasan ku da na haifa kadai ne baza ku goranta mata asali ba, baza kuma ku kyamace ta ba, za ku riketa ne da amana ko da raina ko babu raina" Abba ya girgiza kai yace "I don't think there is any means da za ace za'a fara neman iyayenta or anything of such a yanzu because it's of no use, ko daga yanda aka yi dumping dinta a wajen nan a ranan ya nuna ba a bukatarta ne kawai, ba a kuma ajiyeta a wajen da niyyar ta rayu har wani ya dauketa ba, a'a an ajiyeta ne kawai ta mutu, ba kuma a jikin masallaci kamar yanda ku ka ji ana cewa aka ajiyeta ba, i don't know who created that rumors, kawai nasan that faithful day na fito kamar yanda na saba zan zuba ruwa a randunan masallaci kafin jama'a su fara fitowa sallahn asubahi, daga inda ake debo ruwan a wani rijiya ne, sai dai babu wani tazara tsakanin inda rijiyar yake da masallacin, a nan gaba da rijiyan aka nannadeta cikin zani har fuskantar sannan aka saka ta cikin kwali kuma aka rufe kwalin da plank ta yanda iskan kirki ma bazai shiga ba, kaga wanda ake son ya rayu ai baza ayi masa haka ba, kuma me imani bazai taɓa yi ma ɗan da ya haifa haka ba, kai koma ba ɗan da ya haifa ba bazai bari ayi ma wani haka ba, tabbacin koma wacece ta ajiyeta bata da imani, bata tsoron Allah sannan azzaluma ce don da niyyar kasheta tayi hakan, ina jan ruwa a rijiyar nan ina jin kamar kukan jariri amma na rasa a ina gashi kukan babu sauti sosai can kasa kasa ake jin kukan, kawai na bayar ko mage ce ke wannan kukan, har sai da nayi sahu uku da ruwan na kasa hakuri na fara duba wajen da torchlight ina neman inda wannan sautin kukan ke fitowa, in takaice maka nafi minti 10 ina dube duben area din daga karshe na lura da kwalin da aka ajiye nesa da rijiyar kusa da wani kwata na karasa na daga plank din, sai ga sautin kukanta sosai, i was shocked don dai anyi wrapping har fuskarta da zani, na kasa taɓa ta gashi babu kowa, duk ana ciki yawanci ba a tashi bacci ba don karfe hudu da rabi ma bai karasa ba a lokacin, tsabar yanda na zama confuse kawai na koma gida gun Amminku, ita ma tana bacci na tasheta nan na sanar mata abinda na gani bakin rijiya, babu bata lokaci ta sako hijab ta biyoni muka dawo wajen, har sannan kuma jaririyar bata daina kuka ba, Ammi bata yi wani tunani ba kawai ta cirota daga kwalin cikin tashin hankali ta warware zanin da aka yi wrapping dinta da shi, a lokacin sai Amminku ta fashe da kuka tana salati, don yanayin da jaririyar ya nuna ba a ma jima da haihuwarta ba tunda ko goge jikinta ba ayi ba, Ammi bata bi ta kaina ba tayi cikin gida da jaririyar nan a hannunta, Ni dai tsabar yanda mamaki da takaici ya isheni jikina yayi sanyi na koma bakin masallaci na zauna ina tunanin wacce azzalumar ce zata aikata wannan abun comfortably babu tsoron Allah a ranta, sannan duniya na kwance lkcn duk bamu san a haifi jariri a yasar shi ba, wannan yasa abun ya tsaya min, ya kuma tsaya ma mutane da yawa a rai, don kafin gari ya waye labari ya karade unguwa har ma da makota an tsinci jaririya a bakin masallaci kamar yanda ake cewa, da Ammi ta gyara yarinyar ta mata wanka sai da nayi kwalla, ita dama tun da ta dauko yarinyar take kuka, fara ce kal jaririyar, she was a cute baby kamar balarabiya, nan dai aka kai ta gun manyan anguwa aka fara shawaran yanda za ayi da ita, kowa dae na tsoron yace zai riketa don ba a san dalilin yasar da ita a walakance ba a bakin kwata, wasu suka bada shawaran a kai ta gidan marayu, a sannan ma gidan Marayun bai yi yawa ba kamar yanzu ina jin ma babu a garin sai anje wani gari, aka dai yarda akaita can gidan Marayun a harhada kudin mota, duk fa ba wai mun san yanda process din yake bane a lokacin sannan bamu sako yan sanda a ciki ba, nan na shigo gida na sanar ma Amminku shawaran da aka yanke akan jaririyar nan, Ammi ta sakar min kuka ta fara hadani da Allah ita dai a bar mata yarinyar zata rike, tunda a sannan Umar was almost 5 years kuma shi kadai ne a gabanmu, after much pleading and begging, har ta hadani da Hajja, Hajja ma ta saka baki a maganar babu yanda na iya ba don raina ya so ba manyan anguwa suka damka ma Ammi jaririyar nan, a ranan kuma tace min ita dai ta saka mata suna MAYRAAH, as at then we were leaving from hand to mouth, nayi ta kokarin nuna ma Ammi baza mu iya da dawainiyar jaririyan ba muma muna fama da kanmu a garin, gashi Ammi ta jima da yaye Umar babu ruwan Maman da zata ba yarinyar which means dole madara za a dinga siya mata kenan, a hakan ma yan anguwa sun harhada tsofaffin kayan yaransu an kawo ma jaririyan, har kudi aka hada da bai taka kara ya karya ba aka bamu, da shi muka fara siya mata madara, ni dai duk hankalina bai nutsu da rikon yarinyar ba kawai ina jin kunya Hajja ne, a ranan na fita naje kasuwa inda nake dako a biyani kafin in harhada yan kudadena in siya kaya marasu tsada in shiga Cameroon in siyar sai inyi wata daya ban gama hada kudin siyan kayan ba wani lkcn duk abinda na samu ma dole da shi za a ci abinci, that same day da muka tsinci Mayraah ina kasuwa from no where sai ga wani bawan Allah ya bani dubu goma daga kai masa kaya mota, imagine 10 thousand 22 years ago, ai kaga ba karamin kudi bane, nayi ta farin ciki na koma gida duk da ko minti talatin banyi da fitowa ba, a washegari sai ga wata dubu uku daga wata Hajiya ita ma na dau mata kaya zuwa mota, let me make this brief, tun daga sannan ba ayi ranan da zan fita ba a min kyauta ba, me yawa, ɗan kadan a haka dai kullum, nan na dinga saran kaya ina shiga Cameroon a kwana biyu uku kaya suke karewa tas ga riba wanda a baya sai inyi sati uku a Cameroon kaya basu kare ba, tun daga samun Mayraah hanyoyin arziki suka dinga bude mana ta ko ina, ta yanda bamu taɓa tunani ba a rayuwarmu, in less than few months ni kaina na tsorata da abinda na tara, nayi ta jin tsoro, haka ma Amminku wanda nasan da bata san halina ba tunani zata yi sata na fara, amma abu sai kara ci gaba yake, harkoki na ta bunkasa kan kace me kafin wata 12 muka tattaro muka dawo kano, kaga kuwa samun Mayraah alkhairi ne a garemu, kuma ko da muka dawo Kano barka kawai ake shigowa yi ma Ammi tunda shekaranmu daya a can muka samu Mayraah, tana wata sha biyu kuma muka dawo Kano, don haka babu wanda ya kawo cewar ba er mu bace Mayraah, ku kanku where very happy bayan dawowarmu don an sanar maku Amminku ta haihu tun bamu dawo ba.... Usman ya ɗaga kai yana kallon Abba jin yayi shiru, Abba ya nisa yace "Ko da wasa mu ma bamu taba zaton akwai randa za mu yi ma 'ya yan da muka haifa tayin auren Mayraah ba don duk daya muka dauke ku gaba daya babu banbanci, amma muna namu Allah kuma na nasa...." A hankali Usman yace "Yanzun ma hakan baxai faru ba Abba, we will continue being the brothers we are to her, for better for worst we will protect her and will always be there for her, babu wanda zai taɓa ta ya kwana lafiya, ko da yau ta samu wani da zai aureta kallon banza idan ya hadasa da ita balle har ya kai ga goranta mata asali zai gane she has a Barrister as a brother and 2 other elder Brothers, not even outsider ko na cikin gida ne yace zai takura Mayraah i in particular can go to any extent na kwatar mata 'yancin ta, i will take that personally i am assuring you Abba, don haka har abada babu aure tsakaninmu da Mayraah, she remains our blood sis" Yana kai wa nan ya mike yace "I want to excuse my self sir" Abba ya gyada masa kai, ya juya ya fice daga parlon Abba ya bi sa da kallo. Maheer ne tsaye dakin Ammi kansa a kasa duk da bacin ran dake tare da shi bai nuna a fuska ba but deep down him he is boiling and yana ta controlling kansa baya son yayi wani magana da zai kara hurting din Amminsa hankalinta ya kara tashi, gwara ya bar ta ma taji da wanda take ciki yanzu, Ammi dai sai goge hawayen da ya ki tsaya mata take maganar ma ta kasa ci gaba da yi, not long ago ta dawo daga gidan Hajja don ko minti sha biyar bata yi da shigowa gidan ba, after a 5 minutes silence tsakaninsu Maheer ya dago kansa yana kallon Ammi yace "Shikenan... Na kuma fahimce ki Ammi, for the meantime Mayraah zata koma gidana...." Ammi ta daga kai tana kallonsa, yace "Eh zata dawo gidana, a nan kuma zata zauna, Hajja don't have any say in this, ba kuma wai don Hajja zata hanata zaman nan gidan Abba bane yasa zata koma gidana don zamanta a gidan nan ma Hajja bata da say cause this is our father's house, ban san irin zaman da za ku fara yi da Mayraah ba idan ta ci gaba da zama a gidan nan shi yasa zan maida ta gidana, don haka gobe zan je gidansu Haseenah in daukota, duk sanda Hajja ta gane kuskuren abinda take kokarin yi fine, zan so ki rabu da ita lafiya, don haka ki ci gaba da yi mata biyayya...." Aunty Mariya ce ta shigo dakin da akwatinta, tana kallon Ammi cikin sanyin murya tace "Toh Ammi, ni zan tafi sai mun yi waya" Kai kawai Ammi ta gyada mata tana share hawayen da ya ki tsaya mata har sannan, Aunty Mariya ta kalli Maheer tace "Zan tafi Maheer" Sauke idonsa yayi yace "Bari in kai ki park Aunty" Fita tayi daga dakin ya juya ya bi bayanta, bayan ya kullo kofar Aunty Mariya na kallonsa cike da damuwa tace "Ku yi hakuri Maheer, kuyi hakuri da duk abubuwan nan dake faruwa, Allah zai daidaita al-amarin nan in sha Allah, sannan nasan Mayraah bazata yi nisa ba, duk inda ta tafi zata dawo a yau da izinin Allah, tunda Hajja tace in tafi gwara in tafi kawai" Shi dai Maheer bai ce mata komai ba, ta fara tafiya ya bi bayanta.
A hankali Mayraah ta bude idonta, ta dinga bin dakin da take da kallo, kwance take saman gado an rufeta da lallausan farin duvet, ta mike zaune da sauri trying to recall where she is, and who brought her here, idonta ya sauka kan alluran dake kan bedside drawer da drugs, cikin few seconds komai ya fara dawo mata, ta cire duvet din jikinta zata sauka daga kan gadon taji kamar an soka mata mashi a kirjinta, dafe kirjin tayi da sauri feeling so much pain, dai dai nan aka bude kofar dakin, ta daga kai ta kallesa, tsaye yayi bakin kofar yana kallonta, can dai ya karasa yana tafiya a hankali ya isa har inda take ya zauna cikin sanyin murya yace "How are you feeling now?" Tun safe sai a yanzu taji kukan da ta kasa yi ya taho mata ta kasa controlling kanta, kamo hannunta yayi yace "Noo pls kar kiyi stressing kanki Mayraah, u need rest" Ta warce hannunta daga nasa cikin kuka tace "Saboda kasan wacece ni shi yasa kake avoiding dina yanzu kake kashe wayarka don baka son...." Dakatar da ita Musharraf yayi yana girgiza kai yace "That is the last thing i will do on earth Mayraah, and mind u tun kafin ke kanki ki san ko wacece ke na riga ki sani, kuma hakan bai sa naji kin canza a zuciyata ba, i switched off my phone for my mental health..." Tace "You are avoiding me because of ur mental health?" Yayi shiru yana kallonta kamar yanda ita ma ke kallonsa, daga fuskarsa kadai zaka gane ya rame, he doesn't even look normal, can ya juya yana kallon side daban yayi kasa da murya yace "Na ba Dr Maheer space ne ya gama maki duk injections dinki da aka yi prescribing, sannan ya kula dake kamar yanda likitan ya umarta, so i had to back off for my sanity" Kallonsa kawai Mayraah take, ya mike tsaye yana facing dinta, hawaye ne kawai ke sauka idonta tace "But that isn't enough to let u ignore me all this while, when u know i will need u the most during this hard time" A hankali Musharraf yace "Kinsan yanzu da aure tsakaninku da Maheer and Usman?" Kallonsa Mayraah take babu ko kiftawa, ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa, ba a dau lokaci ba ya dawo dakin da plate din abinci da ruwa, ya ajiye mata kan bedside drawer yana kallonta yace "Mayraah" Ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta, zaunawa yayi kusa da ita yayi kasa da murya yace "I am sorry Mayraah.... u know i love you soo much, ina sonki fiye da yanda kike zato, amma the thought of Maheer made me sick for all the 3 days da kika ji wayata a kashe, i became insecure zuciyata na ta raya min abubuwa da yawa, kilan saboda abubuwan nan da suka faru Abba can just decide to get u married to Maheer or Usman, the thought of that nearly took my life this 3 days, Mayraah I can't imagine loosing u, i don't know what will become of me idan na rasa ki, kiyi hakuri ki yarda da ni mu je a daura mana aure, i promise to give u all the love in this life, i will protect you till my last breathe, u will neva regret trusting me" Mayraah na share hawayen dake sauka idonta a hankali tace "I have to because i have no option, a yanzu ina ga bani da kowa kuma bani da inda zan je, i am all alone in this life" Musharraf ya girgiza kai ya kamo hannunta yace "You are not alone Mayraah" Tana kallonsa cikin rawan murya tace "I don't know what is happening but i overheard my grandma telling Ammi to choose between i and her, she said....." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai, Musharraf ya jawota kusa da shi yace "It's okay Mayraah, baki ji ta bane da kyau, u misheard her, yanzu ki ci abinci ki sha magani, it's almost magrib" Yana fadin haka ya dauko abincin ya fara bata a baki, cokali daya ta ci ta girgiza masa kai da kyar tace "Bazan iya ci ba, my chest is aching" Yace "Bari in kawo maki shayi" Tashi yayi ya fita daga dakin, ta koma ta jingina da gadon all this while sai yanzu ta ɗan ji ta samu relieve, bayan some minutes ya dawo dakin da cup din shayi ya mika mata yace "I diluted it, babu zafi" Amsa tayi ta fara sha, ya dauko mata magungunan yana bude mata, tana gama shan shayin ta amshi maganin ta sha, yace "Zan je masallaci in dawo, kiyi alwala kema kiyi sallah" Ta gyada masa kai ya mike ya fita daga dakin.... Ko da Musharraf ya dawo Mayraah har tayi sallah, ya ajiye mata yoghurt da ya shigo mata da shi ya zauna yana kallonta yace "Are you feeling pain any where?" Ta girgiza masa kai, a hankali tace "But what will be the outcome of my final exams?" Yayi shiru yana kallonta, can a hankali yace "Shouldn't we get married first before thinking of that Mayraah...." Mayraah ta zuba masa manyan idanuwanta, bude side drawer yayi ya ciro wayarsa ya kunna yace "Let me make a call, if possible in ga ko za mu iya zuwa Abuja gobe..." Ita dai kallonsa kawai take, yana kunna wayan bayan ya gama booting kira ya shigo wayar, ya daga kai ya kalleta ganin me kiransa, hade rai tayi ganin Dr Maheer a gaban screen din......
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
0 Comments