Mayraah Page 20 Complete Novel By Khaleesat Haiydar
Page 20
Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga Sister Nafisat Sanda (Mom twins🥰) Allah Ubangiji ya raya mana twins mu taho biki Sakkwato muna daddaga shoulders😁 Hajiya Safiyya Usuman🤪 (Ummu Sultan) 5 gbosa for you, Allah ya karo arziki ki bude plazan kayan yara a titin anguwanku, Allah ya raya mana Noor in fara tara kayan kitchen 😁
My lovely fans ina maku fatan alkhairi for always being there for me, Allah ya raya maku zuri'a🥰
Mama Ladi ta saki salati ta mike ta dafe gwiwowinta tana kallon Hajja kamar ranan ta fara ganinta tace "Yau mun shiga uku, Me ya sameki haka Hajja? Ko dai ɓatan hanya kika yi ba nan zaki zo ba?" Hajja ta dakatar da ita tana huci tace "Kee babu ruwanki a maganar nan ki kama gabanki kar ranki ya baci Ladi, magana ce nake yi tsakanina da 'ya ta" Mama Ladi ta mike zumbur ta wangale hannu tace "Ba lafiya jama'a, to amma dai a yanzu ai kowa yasan ba Ammi ke da iko da Mera ba a gidan nan, sai dai in kije ki samu Mamuda dama bai fita ba, kije dakinsa ki samesa ki zazzage masa duk abinda ke ranki, haka kawai mata muna zaman zaman mu baza ki zo nan ki daga mana hankali ba gaskiya, ki tafi can dakin Mamuda kice ya maida Mera jikin masallacin da ya tsintota tunda shi ya tsintota ai ba Ammi ba, babu ruwan Ammi a wannan maganar gaskiya, ita umarnin mijinta ta bi take rike da Meran har yau don zaman lafiyanta da mijinta, in kuma kashe mata auren zaki yi ta koma gidanki to sai mu ce Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, don wannan hanyar kashe mata aure kika dauko" Aunty Mariya was speechless and shock, gaba daya jikinta yayi sanyi, ta ma rasa tunanin da zata yi balle tace wani abu, to in ma tana da abun cewan ba dai a gaban Hajja ba, don tsaff sai Hajja ta iya tsine mata, Ammi kam dawowa tayi kamar an dasa ta a wajen don ko kifta ido bata yi, that was the least she was expecting from Hajja, she was still finding it hard to believe Hajja ce yau ke fadan wannan maganan, is this really Hajja, her eyes where soo dry tsabar yanda maganar ya zo mata a bazata ita da hawaye bai da nisa daga idonta, kallon Hajja kawai take babu ko kiftawa, Hajja na kallon Mama Ladi tana nunata da ɗan yatsa take cewa "Nace ki cire bakinki a batun nan Ladi kada ki kai ni bango, ki cire bakinki a abinda ya shafi zuri'ata tunda baki da alkhairin da zaki fada, in dai har akan Mayraah abubuwa za su yi ta faruwa haka suna caɓewa a zuri'ata to na yanke shawara Hajara ta zabi ko ni ko ita kawai, ehh ta zabi ko ni ko ita Mayraahn, bazai yiwu a kan Mayraah a kusa nakasa Badiyya ba sannan har yau babu wanda yaje yace mana ci kanku balle ya duba halin da take ciki daga ku har shi munafukin da yayi dukan, bazai yiwu akan Mayraah 'ya yan Hajara su dau ƙaran tsana su dora ma Badiyyah ba, basu da makiyiya sama da Badiyya a duniya, sannan yanzu kuma a kan Mayraah banga dalilin da zai sa Maheer ya kora matarsa da duka duka kwananta daya a gidansa, wai fa duk saboda Mayraah, to ita Mayraahn nan duk abubuwan nan dake faruwa duk ta dalilinta alkhairi ce a garemu kenan?? ai a ganina an mata mai wuya tunda har aka riketa aka ciyar da ita kawo yanzu da tasan kanta, wani irin karatu ne bata yi ba gashi za a yaye su a jami'a kwanan nan, don haka bazan zuba ido in ga familyna na neman lalacewa akan wata da babu abinda muka hada da ita ba a duniya sai don zuciya irin ta musulunci da ya sa muka sakota cikinmu ba tare da mun kyamace ta ba, nayi hakuri na kauda kai, na nuna komai ba komai bane yau shekara ashirin da biyu kenan, tun daga kan yanda ake banzatar da Badiyya da lamarinta a kan yarinyar nan ma ai yaci ace na dau mataki, amma ban yi haka ba saboda zuciyar musulunci, don haka duk sanda Hajara ta yanke shawara sai ta zo gida ta sameni, Ko ni ko Mayraah, bazan mutu in bar baya da ƙura ba..." Hajja na kai wa nan ta nufi kofa fuuu ta fice daga parlon, Mayraah dake tsaye tun shigan Hajja parlon Ammi kuma duk ta jiyo abinda Hajja ke cewa ta juya da sauri ta nufi dakinta ta kulle ta jingina da kofa tana maida numfashi.... Sai a sannan hawayen tashin hankali ya kawo idon Ammi tana kallon Aunty Mariya da tayi tagumi tana furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a ranta, Mama Ladi na tafe hannu tana zare ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una lalacewa ta samu Hajja, dama Hausawa sunce ba farkon ba karshen, yanzu dama haka Hajja ta koma ni ina can Karaye ban sani ba?? me ya sami yayata ta lalace da mugun hali haka?" Tana kai wa nan ta fice daga parlon ta nufi dakin Usman, Aunty Mariya tayi karfin halin cewa "Ammi ki kwantar da hankalinki, nasan cikin bacin rai Hajja tayi maganganun nan she doesn't mean it har ranta...." Kasa ci gaba Aunty Mariya tayi hawaye na sauka idonta tana tausayin yayar tata, Ammi dai ta rike kanta hawaye na zarya a idonta tana jin zuciyarta na mata zafi, har sannan maganganun Hajja ne ke kai kawo a kunnenta, Aunty Mariya ta koma gefenta cike da karfin hali ta rungumota tace "Don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki Ammi...." Sai a sannan Ammi ta fashe da kuka sosai... Mayraah ta fi minti bakwai tsaye jikin kofar dakinta ta kasa motsawa daga wajen, her eyes were soo dry, lkci daya taji kirjinta yayi mata nauyi sosai kamar an daura mata ƙaton dutse, ta kasa ci gaba da tsayuwa ta lallaba ta koma gefen gado da kyar ta zauna hoping zata samu relieve din kirjinta da ya riƙe, bata ji ya mata saukin azaban da yake mata ba, daga karshe ta lallaba ta daure ta tashi ta tafi gun da Hijab dinta yake ta dauka ta sa, ta ciro Nikab dinta ma ta saka sannan ta dau handbag dinta ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar don taji ana ta knocking din dakin Usman, leka corridor din tayi taga Mama Ladi tsaye sai bubbuga kofar Usman take ba kakkautawa, rufe kofarta tayi making sure it made no sound, ta jingina jiki tana jin kamar she is beginning to find it hard to breathe normal, bayan wani lokaci taji Mama Ladi a fusace tana cewa "Kai ya za a dinga buga kofarka ka ki tashi kamar me baccin mutuwa, wannan wani irin baccin asara ne Usman, ina ma ka ga ta bacci gida ya kacame ba lafiya ta ko ina" Mayraah taji Usman yace "Me ya faru?" Mama Ladi ta shige dakin tana cewa "Ba maganar tsayuwa bace ai" ya bi ta ciki sannan ya kulle kofarsa, Mayraah na jin haka ta bude dakinta a hankali ta fito, da sauri ta sauka downstairs ta fita compound, cikin few minutes sai ga ta a bakin titin gidansu, adaidaita sahu ta tare ta shiga bayan ta sanar masa inda zai kai ta... Duk da tafiyar da Mayraah tayi zuwa department din nasu ba wani me nisa bane, amma da kyar ta karaso saboda numfashinta da take ji yake sarke mata, she was so tired, bata karasa har bakin department din ba don ma kar wani ya ganta ya ganeta ta nemi karkashin wani bishiya me dauke da gossip chair ta zauna tana maida numfashi, she sitted there for 3 good hours, amma babu alamar shigowar ko daya daga 3 cars da yake zuwa makarantar da su, ganin it's almost pass 12 tayi karfin halin mikewa, zuwa yanzu ita kadai tasan me take ji a duk jikinta da kirjinta, ga wani jiri dake dawainiya da ita, tafi minti sha biyar tsaye bakin titin makarantar tana tunanin inda zata je, daga karshe ta tsayar da adaidaita sahu ta shiga ta sanar masa inda zai kai ta.....
Bayan tafiyar kusan minti talatin mai adaidaita sahun ya tsaya dai dai inda Mayraah tace masa ta sauka sannan ta basa kudinsa, a hankali take tafiya zuwa gate din gidan, she leaned against the gate for almost 5 minutes kafin tayi knocking, gajiya tayi da kwankwasa gate din don babu alamar za a bude, bata ma san ko da mutum a gidan ba at first, she is soo tired and sick everywhere, kawai daurewa take ga rana me zafi, tana ta tsaye nan don ko inda zata zauna babu, don ma dai tun zuwanta bata ga kowa ba a street din and that made her more comfortable to keep standing by the gate, masallacin dake next street taji ana kiran sallahn azahar, ta jingina da gate din gidan ta rufe ido, ji tayi ana unlocking gate din after almost 15 minutes, ta gyara tsayuwarta ta koma baya da sauri gabanta na faduwa don bata ma san wanda zata gani ba, aka bude gate din at last, kallonta yake kamar yanda take kallonsa ta cikin Nikab din fuskarta, he looks so surprise and perplexed seeing her, ya bi street din da kallo da mamaki yace "Mayraah!" Ita dai bata ce masa komai ba ta sauke idanuwanta daga kallonsa, da sauri ya kamo hannunta zuwa cikin gidan ya kulle gate din ya dage Nikab din fuskarta yana kallonta, ganin yanayinta and how she is beginning to heave yace "Are you okay??" Girgiza masa kai kawai tayi, bai sake cewa komai ba yana rike da hannunta ya nufi cikin gidan da ita da sauri, ko karasawa entrance din parlor basu yi ba Mayraah ta fara ganin gidan na juya mata bata sake sanin inda kanta yake ba daga nan kuma.
Maheer ne tsaye yana kallon Aunty Mariya sounding so pissed off yace "Aunty I think babu ruwan kowa da duk wani harka da ya shafi gidana ko matata, idan ma sakin Haseenah nayi it's my decision and i am old enough to make decisions for myself babu ruwan wani, ai ba wani ya bani shawaran aurenta ba so babu wanda zai bani shawaran yanda zan zauna da ita banda mahaifiyata ko mahaifina, ina ruwan Hajja da abinda ya shafi gidana har zata daura ma Mayraah? I don't think wannan ne kaɗai dalilin da yasa ta zo gidan nan tayi abinda tayi, there is definitely more to that, Kuma in har tace Ammi bazata kara rike Mayraah ba mu za mu riketa don kanwar mu ce har yau har gobe and this is our fathers house, beside ko gidana Mayraah zata zauna nobody is going to question that, dalilina kuma na maida Haseenah gida still remains between i and her, wannan tsakanina da ita ne babu wanda ya shafa, kuma babu ruwan Mayraah a mayar da Haseenah gida da nayi" Usman dai na tsaye ya rungume hannu fuskar nan tasa a murtuke tsabar bacin rai ko magana yaki yi, Aunty Mariya dai sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, gaba daya ta ma rasa abinda zata ce, tun dazu Ammi dai ta kama hanyar zuwa gidan Hajja and this is 12pm bata dawo ba, wa ya sani ko zuwa zata yi ta ce mata ta amince babu ita babu Mayraah din kamar yanda Hajja ta bukata, Mama Ladi na tafe hannu tace "Kai in fa za ku fito fili ku buda ma ubanku abinda ke faruwa ku fito, babu wani zancen nuku nukun da za a mashi wannan karan, Hajja ce ta zo har nan da sassafe ko tashi daga bacci bamu yi ba tace zata ɗaga ma Ammi mama idan bata sallama Mera ba ta shiga duniya, fitar Hajja ke da wuya aka nemi Mera ko sama ko kasa aka rasa alamar yarinyar ta ji duk abinda Hajja ta fada a gidan nan, iyakar maganar fa kenan, duk da nasan Mera dole ta dawo duk inda ta tafi tunda babu dangin uwa balle na uba a duk inda za ta, yarinta ce kawai yasa ta bar gidan nan amma nasan tana hango magariba zata dawo shi yasa hankalina bai wani tashi ba, wancan lokacin da ta gudu ai tana ganin babu sarki sai Allah sai gata ta dawo da asuban fari, wa ya sani ma ko a titi ta kwana ranan, to yanzun ma muna zaune za ku ga ta dawo wujiga wujiga wanda ke da dangi ma ya ya kare idan ya shiga duniya balle ita da aka tsinta bakin masallaci a tsumma, sannan a buda ma Mamuda cewa Badiyya ce ta ruguza auren Mera, in ma Shari'a zai yi da ita bismillah dama ya haifi lauyan da zai tsaya masa ai, ita kuma Ammi karshen biyayya idan ta dawo muga tana watsi da kayan Mera titi taga ita ma irin koran da Mamuda zai mata, ai Mamuda ke da iko da gidansa ba ita ko uwarta ba, ko shi da 'ya yansa kadai sun isa su rike Mera, sannan nima nan ban ki in riketa in samu lada ba, sai in koma karaye in tattaro sauran kayana in dawo kawai, Mariya kuma ku bar ganin tana matsar kwalla a nan muna barin parlon nan ita ma zata saɓa gyale ta bi bayan er uwarta zuwa gidan uwarsu duk kukan munafurci take yi a nan, a yanzu gatan Mera Mamuda sai ni da ku kawai" Ficewa Usman yayi daga parlon ya tafi na baƙi don Abba na can, zaune ya tadda Abba shi kadai a parlon, tun bayan fitar Ammi daga parlon zuwa gidan Hajja bai motsa daga inda yake zaune ba don Ammi bata boyesa masa duk abinda ke faruwa ba, bai taɓa tunanin abubuwa will turn out this way at the end ba, da sun san haka abubuwan za su kasance da har ita Mayraah din baza su boye mata wacece ita a garesu ba baza su boye mata ba su suka haifeta ba, iyaka su sakaya suce iyayenta hatsari suka yi suka mutu suka tsinceta ita kadai a motar, and sun yi bakin kokarinsu basu gano relatives dinta ba, da hakan suka yi tun farko da abubuwa sun tafi smoothly, all this while Abba avoiding din Mayraah yake don bai san da idon da ma zai kalleta ba, gani yake daga shi har Ammi failed her, they disappointed her don ta taso da mentality din su suka haifeta amma all of a sudden rana daya taji ba su ne iyayenta ba, she is going through all this because of them hakan na damun Abba sosai, yanzu ko nan gaba aka samu wanda zai aureta tabon nan na rashin asali bazai taɓa goguwa a tare da ita ba, kawai he is just acting like everything is okay but deep down him he feels so sorry for Mayraah and he regret their actions, ya ma ga kokarinta duk da yasanta to be a very strong gal tun tasowarta, to yanzu ga kuma wani matsalan da Hajja ta billo da shi, Ammi kuma duk duniya babu maganar wanda take ji bayan shi da yake mijinta sai Mahaifiyarta, and her mum first in everything.... quite alright ba don Hajja ba da gidan Marayu zai mika Mayraah shi da yan anguwan a ranan da aka tsinceta duk da yanda Ammi ta nace masa a lokacin ya bar mata ita amma yaƙi har sai da Hajja ta saka baki... Bayan wani lokaci Abba ya daga kai yana kallon Usman da ya shigo parlon, Usman ya nemi waje ya zauna, Abba dai bai ce masa komai ba, after few seconds Usman yayi karfin halin cewa "Yanzu a ina za mu samo Mayraah?" Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya calmly yace "Zata dawo, she will come back in sha Allah, babu inda zata je" Usman ya mike yace "But It's over 3 hours da fitar ta gidan nan fa, who knows the condition she is now??" Abba ya jinginar da kansa da kujera kamar bazai ce komai ba, can yace "Sit Usman" Usman ya koma ya zauna, Abba yace "Ga wata alfarma da nake nema gun ka Usman" Usman ya daga kai yana kallonsa, Abba ya nisa, cikin calm voice yace "Usman ina son hada aure tsakaninka da kanwarka Mayraah, i know u will protect her as ur sister, ur wife and as the orphan dat she is"
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788