Mayraah Page 19 Complete Novel By Khaleesat Haiydar
Page 19
Haseenah ta dinga bin motar Maheer da kallo ko kwakkwaran motsi bata yi a inda take tsaye har taga ya bar layin nasu, bayan few seconds ta hadiye wani abu da ya makale mata a makogwaronta da kyar, gani take kamar fa mafarki take ba gaske ba, ta kikkifta ido ta bude still dai ta ganta tsaye a kofar gidan nasu, nan fa ta tabbatar ba mafarki bane da gaske ajiyeta Maheer yayi a gida, tayi karfin halin juyawa ta kalli gate dinsu dake a kulle, bata san sanda ta fara tafiya ba da sauri ta bar bakin gate din tana tafe tana harhade hanya kamar mara gaskiya, da hijab dinta ta dinga rurrufe fuskarta don kada wani a layin ma ya ganta ya ganeta, a haka har ta bar layin gaba daya ta isa bakin titi, zufa ne ke keto mata a goshi ga cikinta dake murda mata, sai a sannan ta daura hannu daya a kai cikin tashin hankali tace "Na shiga uku" tunanin inda zata nufa yanzu ta fara yi, Zaliha ta fado mata, sai kuma ta girgiza kai da sauri don tasan tana zuwa gidansu Zaliha yanzu dole su hadu da mamar Zaliha, matar da wuni tayi a gidansu ranan bikinta, gashi banda wayarta babu ko sisi a hannunta, gefen ta koma jikin wani shago ta shiga kiran layin Badiyya, har ya katse bata daga ba, ta sake kira tana addu'ar Badiyya ta rufa mata asiri ta daga kiran don ita kadai ce mafitar ta a yanzu, Badiyya na dagawa kamar warce ke cikin maye tace "Account din zan turo?" Sai a sannan Haseenah taji hawaye ya cika idonta, ta fashe da matsanancin kuka tace "Badiyya na shiga uku, don Allah kina ina yanzu?" Badiyya dake kwance bakinta yayi suntum ta mike zaune da kyar don duk jikinta ciwo suke mata wai a haka Hajja ta kai ta chemist an mata allura an bata magani, Badiyya tace "Me ya faru??" Cikin kuka Haseenah tace "Ni dai don Allah gaya min kina ina, in fara barin nan kafin wani da na sani ya gan ni, in ma Bichi kike sai in taho kawai yanzu" Badiyya ta zaro ido tace "To fa... To me ya fito dake? Jiya fa muka kai ki Haseenah" Haseenah ta rushe da sabon kuka tace "Ni dai ki fara gaya min inda zan sameki Badiyya" Badiyya tace "Ke ni fa gani a gida ba lafiya fa" Haseenah tace "Innalillahi, Badiyya kin dai san bazai yiwu in zo gidan ba kada kakarku ta gan ni ko, Badiyya gidanmu Maheer ya maido ni yanzun nan" Badiyya ta zaro ido tace "Gidan ku kuma? Garin yaya?" Cikin kuka Haseenah tace "Wallahi, yanzu haka gani a junction din gidanmu na rasa inda zanje, gashi ina tsoron kada wani ya gan ni, ko kuma wani ɗan gidanmu ya zo wucewa" Badiyya tace "To gashi ni bazan iya fitowa ba bakina yayi suntum baki ji yanda nake maganan ba ma, sannan duk jikina yayi tsami ko daga hannu da kyar nake yi wllh, da sai ince mu hadu a hotel, amma kawai yanzu ki samu adaidaita sahu ki taho idan ya so sai in lallaba in fito mu shiga gidan Maman Bala, wannan gidan dai da nake shiga in canza kaya wani lokacin in za mu fita" Haseenah ta gyada kai da sauri tace "To, to gani nan zuwa yanzun nan" Daga haka ta katse wayar ta tsayar da adaidaita sahu ta shige da sauri tana zazzare ido ta gaya masa inda zata. Suna isa layin Haseenah ta kira Badiyya, babu bata lokaci Badiyya ta daga kiran, Haseenah tace "Gani a kofar gidan, don Allah ki fito masa da kudi babu ko sisi a hannuna" Badiyya tace "Toh gani nan" Hajja da ta gama dama ma Badiyya kunu kenan ta juyo tana kallonta da mamaki tace "Ina kuma za ki Badiyya?" Da kyar Badiyya tace "Zan ɗan motsa jiki na ne ko zan ji dama dama, daga nan sai in shiga gidan Maman Bala" Hajja tace "Ki shiga gidan Maman Bala a wannan yanayin Badiyya, a'a da dai kiyi hakuri ki koma ki kwanta ga kunun na dama maki" Badiyya tace "Ke dai ba ruwanki, tunda kika ga zan fita ae zan iya ne" Daga haka ta fice daga parlon Hajja ta bi ta da kallo. Badiyya ta ba mai adaidaita sahu kudinsa tana kallon Haseenah da ke ta hawaye tace "To wai me kika masa haka? Ko da yake mu je gidan Maman Balan tukun" tana dingishi suka shiga gidan Maman Bala tare da Haseenah da ko lura da jikin Badiyya da bakinta bata yi ba tsabar tashin hankalin da take ciki, Dakin yaran Maman Bala suka shiga Badiyya ta zauna tana kallon Haseenah tace "Amma Maheer mahaukaci ne, me kika masa har yake da mind din mayar dake gida daga tarewarki jiya??" Haseenah ta zube kasa ta fashe da kuka sosai tace "Na shiga uku Badiyya, babban tashin hankalina kar ma Mumy ta samu wannan labarin, wallahi nasan kasheni kawai zata yi" Badiyya tace "To kin ki gaya min me ke faruwa, sae kuke kuke da kame kame kike, wani abun kika masa ne?" Haseenah ta hadiye wani abu da kyar tana nazari, ita dai tasan ko karen hauka ya cijeta bazata yi gigin gaya ma Badiyya da kowa yasan bata da sirri abinda ya sa Maheer ya maida ta gida ba, can dai tayi karfin halin cewa "Wai daga yarinyar nan Mayraah sun zo dazu da safe na nuna masa bana bukatarta a gidana shkkn fa Badiyyah, shkkn Maheer ya maida ni gida" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Badiyya ta rike haɓa cike da mamaki tace "Lallai yarinyar nan ta zama annoba a al'umma, saboda ita fa Usman yayi min wannan dukan jiya da daddare a gidansu, Allah Allah nake in samu kaina in san ta inda zan billo ma matsiyaciyar, yanzu kema a kanta aka maida ke gida??" Sai a sannan Haseenah ta kula da yanda halittar Badiyya ya canza gaba daya, amma da yake ba shi ne gabanta ba bata bi ta kan hakan ba sai kuka take, cikin shesshekan kuka tace "Badiyya ki taimaka ki gaya min yanda zan yi, gaba daya kaina ya ƙulle, wallahi kasheni yan gidanmu za su yi in suka samu wannan labarin, zuwa fa kawai yayi ya ajiyeni a bakin gate dinmu daga fita mu siyo abinci a eatry, ashe yasan plan din da ya hada min" Badiyya da taji zuciyarta na tafarfasa tace "Tashi mu shiga wajen Hajja, yanzun nan kuwa zata kira uwarsa...." Da sauri Haseenah ta rikota tana zare ido tace "Don girman Allah ki rufa min asiri bana son kowa yasan abun nan da ya faru banda ni da ke, na yarda dake ne yasa na zo har nan na sameki" Badiyya ta buda baki tace "To yanzu ya kike son ayi? In ba wajen Hajja za mu je ba ta kira uwarsa ni kinga da wani abu da zan iya yi a nan? Ai dole kuwa uwarsa tasan abinda yake faruwa" Haseenah ta girgiza kai da sauri tace "Aa gaskiya ni dai nace maki bana son kowa ya sani, let sort this out without involving anybody" Badiyya ta taɓe baki tace "Cabb, ashe kuwa baza muyi sorting dinsa ba har abada, an gaya maki suna jin maganar kowa banda na uwarsu ne? Ai in ba Ammi bace ta saka baki a maganar nan wllh Maheer bazai saurari kowa ba, ke ma dai da nacin ki sai da na nuna maki illan auren Maheer kika ki saurarata to yanzu ga irinta nan daga kwana daya ya koro ki gida" Haseenah na goge hawayen da yaki tsaya mata tace "Ni dai Badiyya ki min alfarma kar ki gaya ma kowa wannan abun, bari in kira Zaliha ta same mu a nan inji ita kuma shawaran da zata bada" Badiyya ta kyabe baki tace "To kuma babu abinda ya shiga tsakaninku??" Haseenah tayi kamar bata ji ta ba tana kokarin dialing number Zaliha.
Wajen karfe uku da wani abu Mayraah na gyara Bedroom dinta don jiya da shekaranjiya duk a dakin Ammi take kwana, yau kuma dakin nata take son ta dawo, aikin kawai take amma ba wai hankalinta na kan aikin ba, tunani kala kala ne cunkus ke yawo a ranta, gaba daya ji take kamar zata yi zazzabi, the fact that nobody is even saying anything to her akan issue din nan dake faruwa ya sa taji ta fara tsanar kowa a gidan, they are all acting like everything is normal, babu wanda ke son tada maganar ko da wasa, it's more like an bar ta a duhu kawai babu wani bayani from anybody and that's beginning to hurt her deeply, ta goge hawayen da ya taru idonta ta tafi jikin window ta tsaya tana kallon waje, Then who is she? Menene asalinta? Why was she dumped right from birth? Me ye laifinta da aka yi abandon dinta tun daga haihuwa? Tunanin hakan yasa taji wasu sabbin hawayen na sauka idonta, bude kofar dakin aka yi, bata juyo ba ta goge hawayen dake sauka idonta da sauri, jin shiru bayan some seconds ta juyo a hankali don ganin wanda ya shigo, ya jingina da kofar dakin yana kallonta yace "Kukan me kike dazu a gidan Maheer?" Kamar baxata ce komai ba, sae kuma ta girgiza kai tace "Babu komai, i just saw my self crying" ya mata wani kallo yace "That's a lie" tayi murmushin karfin hali tace "Da gaske nake yaya, babu komai" Zai yi magana aka bude kofar dakin ya koma gefe, Aunty Mariya ce ta shigo tana kallonsa tace "Kai Mama Ladi na ta nemanka tun dazu fa" Ya hade rai yace "Kai, gaskiya this old woman is stressing me seriously, me kuma zan mata?" Aunty Mariya tayi dariya tana kallon Mayraah tace "Hajiyata ban ga kin fito kin diba abinci ba har yanzu, ko kawo maki zan yi" Mayraah tayi murmushin karfin hali tace "Zan zo in diba Aunty" Aunty Mariya tace "Better" daga haka ta juya ta fita dakin tana cewa "Kai kuma bari in je ince ma Mama Ladi kace tana damunka" Bai ce mata komai ba ya maida dubansa kan Mayraah yace "Je ki debo abincin" yana fadin haka ya juya zai fita tace "Yaya ka ara min wayarka don Allah" ya juyo yace "Ina naki wayar?" Tace "I lost it" Ya ciro wayarsa a aljihu ya ajiye mata gefen gado sannan ya fita daga dakin, ta karasa ta dau wayar ta zauna gefen gado ta fara dialing number Musharraf, a ranta ta fara addu'ar Allah ya sa ya kunna wayar yanzu, amma unfortunately aka ce mata a kashe, nan da nan hawaye ya cika idonta damuwarta ya karu a kan na da, what is happening? Baya son magana da ita ne yake kashe wayarsa kenan, Kwanciya tayi edge din gadon hawaye me zafi na sauka idonta. Karfe biyar Mayraah ta shigo parlon Ammi ta dalilin kiranta da ta yi, tun da ta shigo Ammi ke kallonta, ita kanta Ammin ta kasa samun nutsuwa har sannan a zuciyarta daurewa kawai take duk abin nan, Mayraah ta durkusa gabanta a hankali tace "Ammi ga ni" Ammi tace "Me za ki girka ma Abbanku?" Mayraah tace "In masa tuwo da vegetable?" Ammi tace "To je kiyi" mikewa tayi ta nufi kofa zata fita suka kusa cin karo da Maheer, ta koma gefe ba tare da ta kallesa ba tace "Sannu da zuwa" daga haka ta fita daga parlon ya bi ta da kallo kafin ya karasa ciki yana kallon Ammi dake kallonsu... Cikin awa daya da wani abu Mayraah ta gama girkin tunda ɗan kadan zata yi dama, Ta dawo parlon Ammi tace "Ammi na gama" Ammi tace "To sannu da aiki" juyawa tayi ta fita, Maheer ya mike yace "Bari in je masallaci in dawo" Ammi tace "Daga can ka wuce gida Maheer, ya zaka fara barin yarinya ita kadai a gida daga kai ta, ai zaka bari ko sati tayi tukunna" Maheer dai bai ce mata komai ba ya fita daga parlon, dakinsa ya tafi ya dau ledan da ya ajiye sannan ya fito ya tafi dakin Mayraah, tana tsaye jikin window tana kallon waje ya sameta, Mayraah ta juya jin an bude kofar dakinta, ya karasa ciki ya zauna gefen gado yace "Ga sakon ki Mimi" Tana kallonsa tace "Na mene?" Yace "Amsa ki duba" Ta sauke idonta sannan ta nufesa ta amshi ledan da yake mika mata, tun bata bude ledan ba ta gane waya ce, tana kallonsa da murmushin karfin hali a fuskarta tace "Nagode sosai yaya" Ya girgiza kai yace "That smile is fake" Dariya ya bata wanda bata san sanda tayi ba, tace "Allah da gaske naji dadi yaya" Yace "Toh kinga wannan is not fake" Murmushi kawai take ta bude wayar taga wanda yafi nata na da ne ma, a hankali tace "Nagode sosai, Allah ya kara budi" yace "Everything for my Mimi" shiru duk suka yi, bayan few seconds a hankali yace "And... sorry about what happened dazu a gidana Mimi, you know i will neva let that slide...." Da sauri Mayraah ta katse sa tace "Aa ni ai ya wuce a wajena har na manta ma" kallonta kawai yake, ta fara bude kwalin wayar, yace "Za a san min tuwon Abban?" Ta kallesa tace "Ohk amma halve, sai in ba Ammi sauran halve din, dama leda uku ne nayi" Yace "Toh bari in dawo masallaci, ki ajiye min a daki" Tace "Toh" Mikewa yayi ya fita daga dakin, Mayraah ta dinga kallon wayar bayan ta bude, sosai yayi mata kyau ba kadan ba and she is so happy about it, taga har da sim card ya siya mata, ta jona wayar a caji sannan ta ajiye kwalin ta tafi bandaki don yin alwala.... Bayan Magrib tana zaune kan darduma aka bude kofar dakin ta daga kai tana kallon wanda ya shigo, ya karaso dakin ya ajiye ledan hannunsa gefen gado, tana kallonsa tace "Ina yini" Yace "Lafiya lau" Tace "Ana ta kiranka a waya" Tana fadin haka ta mike ta tafi ta dauko masa wayarsa da ya bata tun da yamma, ya amsa ya juya ya fita, Mayraah ta dau ledan da ya ajiye mata taga kwalin waya ne a ciki, ta buda ido da mamaki tana juya kwalin, exactly irin wanda Maheer ya siyo mata dazu color ne kawai daban da wancan, ajiyewa tayi gaban mirror ta fita dakin ta sauka downstairs, abinci ta saka ma Maheer kamar yanda yace mata, ta kai dakinsa, zaune ta gansa dakin yana kallo a laptop, yayi pausing movie din ta karaso ta ajiye masa abincin a gabansa tace "A kawo maka tea ne?" Yace "No... thanks Mimi" Ta mike zata fita yace "Ke kin ci abincin?" Tace "Aa anjima" zata fita dakin sai ga Ammi, Ammi tace "Wai Maheer baka tafi ba har yanzu?" Maheer yace "Ammi wai korata kike ne?" Ammi tace "Eh koranka nake, wannan wani irin abu ne haka? Kai in kanwarka aka ma haka zaka ji dadi?" Ya kalli Mimi dake tsaye yace "Aa bazan ji ba gaskiya, bari in gama cin abincin in tafi Ammi" Ammi tace "Gaskiya bana son haka, kar ka sake zuwa min gidan nan kwana kusa, ya zaka fara barin er mutane ita kadai daga kai ta jiya? Don't u have conscience" Muryar Mama Ladi suka ji tana cewa "O'o Allah, O'o Allah, ba fa yarinya bace amaryar nan da zaki wani daga hankalinki haka a kan an bar ta ita kadai a gida Ammi, jiya fa da muka je na kalli idonta da kyau wllh ba yarinya bace, da kyar in ma bata girmi Mashir din ba, ni dai nayi ta mamakin a inda ya samota har yaji sha'awan aurenta, ke fa baki mata kallon da na mata ba jiya, don haka kawai ki ja bakinki kiyi shiru in baki san abu ba" Ammi dai bata ce mata komai ba ta juya ta fita daga dakin Mayraah ta bi bayanta, Mama Ladi na kallon Maheer dake cin abincin da Mayraah ta kawo masa tace "Kai ko kamar wanda aka ma rufa ido, maimakon ka samu yarinya er dai dai warce bata wuce Mera ba zaka kare da uwar mata haka Mashir? Ko kai baka ganta ba wani saɓar saɓar da ita sai uban mazaunai, kyan fuska kawai gareta fa shi ma kamar mai ta shafa, wannan haihuwa daya biyu zata sukurkurce ta fashe, don irin kiɓan kazantar nan zata yi da tayi haihuwa daya, wanda da ta gifta zaka ji doyi" Mama Ladi ta kyabe baki tace "Allah dai yasa kada Usuman yayi irin wannan zaben tumun daren, ya samu yarinya er dai dai abunsa kamar Mera" Murmushi kawai Maheer yayi yana cin abincinsa, Mama Ladi ta juya ta fice daga dakin. Sai da Mayraah ta fara zubo ma Ammi abinci ta kai mata parlonta sannan ta tafi dakin Usman. Ya ajiye wayar da yake yace "Ya aka yi?" Tana jan fingers dinta tana tsaye jikin kofar dakin tace "Thank you so much for the phone yaya, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen, any other thing?" Ta girgiza masa kai tace "Kawai godiya zan maka dama" Yace "Accepted Mimi" Tayi murmushi ta juya ta fita daga dakin.
Da gudu Haseenah ta shige bandakin yaran Maman Bala jin muryar Hajja tana sallama a tsakar gida, Maman Bala ta fito tana amsa sallaman tace "Sannu da zuwa Hajja" Hajja tace "Allah sa dai nan Badiyya ta shigo Sahura" Maman Bala tace "Ehh gata can dakinsu Bala kuwa" Hajja ta nufi dakin, Badiyya ta hade rai tace "To ke Hajja meye na biyoni don Allah kamar wata er yarinya" Hajja tace "Ayya naga kunun har ya huce kin san flask din nawa ya fashe balle in juye maki a ciki" Badiyya tace "Toh ki tafi gani nan zuwa ni dai" Hajja tace "Toh" Daga haka ta juya ta fita, Haseenah ta fito tana zare ido kamar warce tayi ma sarki karya, Badiyyah tace "Yanzu da magariban nan kice zaki kama hanyar Zaria Haseenah, to wai ma wani waya kike da baza kiyi a gabana ba sai kin wani fita tsakar gida, in haka ne meyasa baki je wajen wanda ku ke wayan da baki son in ji ba, ina fama da kaina na fito saboda ke amma don munafurci sai ki wani dinga fita kina kus kus a saya" Haseenah ta marairaice tace "Wallahi ba haka bane Badiyya, duk bayanin da na maki nake yi a wayar da kika ga ina yi, Coursemate dita ce Fatiha fa" Badiyya dai ta kara kyabe baki ta dauke kai, Haseenah tace "Kuma ai da ban yarda dake ba bazan zo wajenki ba Badiyya, yanzu dai bari in maki transfer ki dauko Atm dinki ki cire kudin ki bani inyi maza in tafi" Badiyya ta mika mata hannu babu yabo babu fallasa tace "Haseenah bani sarkan nan da dankunne zanje kasuwan da kaina in siyar" Haseenah ta hadiye wani abu da kyar tace "Yana fa wajen me siyarwan account number kawai zan tura masa ya saka maki kudin wllh, hidimar bikin nan da ake ta yi ne yasa aka samu delay, yanzu dai don Allah gobe za mu yi maganar gold din ta waya, ki tashi muje ki ciran min kudi a account dinki inyi maza in tafi, zan tura maki dubu talatin yanzu" Badiyya na girgiza kai irin ba mutuncin nan tace "Gaskiya idan goben yayi da kaina zan je shagon me gwal din na gaji kuma haka, aban gold din ko kuma aban kudin" Haseenah tace "Ehh goben sai in baki kwatancen wajen mutumin ki je, ai sananne ne a kasuwan" Mikewa Badiyya tayi tana dingishi suka fita daga dakin Haseenah na biye da ita, Badiyya tayi ma Maman Bala sallama suka bar gidan, suna isa gate din Hajja Badiyya tace "Kinga kawai muje gun me POS din ki masa transfer ya baki kudin don ina shiga gida yanzu Hajja zata iya biyoni waje idan nace zan sake fitowa, kuma kince baki son tasan komai" Haseenah tace "Gaskiya kam, wannan sirri ne tsakanina da ke" Suna karasawa gun me POS Haseenah tayi transfer din aka bata cash, Tace "To sai mun yi magana Badiyya, ina isa Zaria zan kira ki" Badiyya tace "Amma dai wajen wa zaki a Zari'a ke da baki da dangin uwa balle na uba a can" Haseenah tace "Haba gobe fatiha zata sameni a Zarian ai, yanzu dai zanje gidan wata Coursemate dinmu ne tukun" Badiyya ta tabe baki tace "Toh Allah ya tsare" Haseenah tace "Ameen" Daga haka ta bar layin da sauri, Badiyya ta koma cikin gida, Hajja na ganinta tace "To kiyi sallah bari in zuba maki kunun" Badiyya ta taɓe baki ta zauna tana kallon Hajja tace "Hajja kin san matar Maheer ce ta zo muka shiga gidan Maman Bala kuwa?" Hajja ta kalleta tace "Matar Maheer? Wani Maheer din?" Badiyya tace "Wallahi kuwa in gaya maki, wai ya korata gida daga dai Mayraah taje gidan ta mata rashin kunya tace bazata dauka ba" Hajja ta dinga kallonta tace "Mayraah ta mata rashin kunya?" Badiyya tace "Wallahi nake gaya maki, ko gaida Haseenar ma bata yi ba da taje gidan tana ta abu Isa isa da gadara, shine Haseenah abun ya ɓata mata rai tace to gaskiya ita bata son haka ya za ayi ta shigo mata gida babu gaisuwa sai kallon walakanci, kar ki dada karki raga Maheer kawai ya dauketa ya maidata gidansu, shine fa ta shiga tashin hankali bata shiga gidan nasu ba ta yo nan hankali tashe" Hajja na tafe hannu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Badiyya tace "Ace Mayraah bata zama annoba ba? Dubi tashin hankalin da take hadawa a family dinmu duk tana neman tarwatsa kanmu ta lalata mana zumunci" Hajja na gyada kai a hankali tace "Wannan gaskiya ne" Badiyya tace "To wannan magana tsakaninmu ne dake, kar ki ce ma kowa komai babu ruwanki, kinga dai ni ga abinda ta sa Usman yayi min don ma Allah ya so da sauran kwanana a gaba, Aunty Mariya na ji tana gani bata kwace ni ba kuma har yanzu ai kinga bata zo gidan nan ba balle ta duba halin da nake ciki, ita kanta Ammin bata kira taji ya jikina ba kuma ya kamata ita ma ace ta zo ta duba ni ai, ai kinga duk babu wanda ya zo, balle Mama Ladi dake ta goyon bayan abinda aka min duk akan wata banza wai Mayraah, yanzu gashi sabon auren da Maheer yayi tana nema ta kashe masa, ai wannan badluck ce a family dinmu wllh, ashe dama babu abinda muka hada da ita shi yasa tun farko na tsaneta jinina bai hadu da ita ba, Ammi tayi ta fifitata a kaina komai ace Mayraah, a gabana Aunty Mariya zata kira sai dai tace a ba Mayraah...." Hajja dai bata ce komai ba tayi shiru, Badiyya ta tabe baki ta mike da kyar ta shiga bandaki...
Washegari da safe Mayraah ta gama shiryawa don tana son shiga school ba don kowa ba sai don Dr Musharraf kilan zata gansa a school din, fitowa tayi zata sauka downstairs taje kitchen don hada ma Ammi shayi, babu wanda yasan zata school a gidan don dama so take sai ta kai ma Ammi shayi kafin tace mata zata je makaranta, a stairs ta hadu da Hajja dake haurowa, tayi murmushi ganinta tace "Ina kwana Hajja" Ko kallonta Hajja bata yi ba, Mayraah ta koma gefe ta bi ta da kallo in shock, Hajja ta nufi parlon Ammi ta bude kofar babu ko sallama, Ammi da Mama Ladi sai Aunty Mariya duk suka daga kai suna kallonta, shiga parlon tayi tana kallon Ammi da kyau tace "Hajara" Ammi ta kasa cewa komai ta dinga kallonta gabanta na faduwa don Hajja bata kiran sunanta kai tsaye sai dai ta kirata da Ammi, Hajja tace "Ina ce dai da yardata kika dau yarinyar nan kika rike har zuwa yau ko? Ina ce Mamuda ƙin amincewa yayi da farko, ni ce nan na karfafa masa gwiwa na rokesa Allah da annabi ya barki kiyi rainon yarinyar tun tana tsumma ko? To a yau nake son ki zabi ko ni ko yarinyar"
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788