Mayraah Page 15 Complete Novel By Khaleesat Haiydar
Maheer yayi kasa da murya yana kallonta yace "I know you to be a very strong lady Mayraah, kiyi hakuri... This is our destiny and we have to accept it with good faith, amma har yau har gobe u still remain our blood nothing can ever change that" Ita dai ta sauke kanta tana goge hawayen da ya fara sauka idonta a hankali, Ya zauna kan kujeran dake kusa da gadon cikin sanyin murya yace "Pls ki daina kukan nan yana taɓa ni, you know i hate seeing you cry lil sis, and tell me if you are feeling pain anywhere??" Ta girgiza masa kai ba tare da ta kallesa ba amma hawayen yaki tsaya mata, yanzu kenan ita ba jininsu bace kowa ya shaida, Maheer ya kamo hannunta yace "I think we can go home now, zan ci gaba da duba ki a can" Mayraah ta zame hannunta da sauri daga nasa sannan ta kallesa jin abinda yace, he felt somehow da tayi hakan, amma dai a hankali yace "Kilan idan Ammi ta gan ki she will feel much better too, kinsan bata da lafiya and taki a kawota asibiti, she is seriously sick" Mayraah ta sunkuyar da kanta, yace "Idan mun koma gida sai kiyi sallahn tunda babu hijab a nan" Ita dai Mayraah tayi shiru bata ce komai ba, yace "Let me go to the Dr's office yayi discharging dinmu" Ta bi sa da kallo har ya fita daga ward din, yana fita ko 5 minutes ba ayi ba Musharraf ya shigo, ta dinga kallonsa har ya karaso kusa da gadon yayi kasa da murya yace "I just finish speaking with My Mami tace in gaisheki da jiki, i told her baza ki iya waya ba...." Mayraah ta sauke idonta daga kallonsa a hankali tace "Yaya Maheer yace za ayi discharging dinmu yanzu mu tafi gida fa" Tana fadin haka ta fashe da kuka cikin rawan murya tace "How will i face them all after all this?" Da damuwa Musharraf yace "No Mayraah bana son kina wannan kukan it's hurting me, and keep in mind that they are still ur family and will remain ur family, ki gode Allah da ya sa hannunsu kika fada kika taso cikin aminci tare da su, and apart from love and care, they also gave u all the goodies of this life, u neva lacked anything tun tasowarki tare da su, they gave u quality education, they took u as theirs without second thought, tunanin haka kadai ya ci yasa ki cire komai a ranki and continue looking at them as ur own family and appreciate them, i only want us to go far away from everyone saboda nasan su kansu a yanzu baza su bari a daura mana aure ba after all this that happened, amma i have no intention in rabaki da su forever....." Bude ward din aka yi Maheer ya shigo ya karaso ciki yana kallon Musharraf da yayi shiru, Maheer yace "We are being discharged now..." Musharraf yace "To maa sha Allah, Allah ya kara mata lafiya...." It took Maheer not less than 10 mins ya kai duk abubuwan da Aunty Mariya ta kawo can parking space ya saka su a booth din motarsa, Musharraf ya cire mata drip din dake makale hannunta ganin kamar ta fada duniyar tunani yayi kasa da murya yace "Nothing about you can ever change in my mind, i still love you more than you can imagine Mayraah, get well soon so we can sort our self out, i think we shouldn't rush matters" Ita dai kallonsa kawai take, Maheer ya dawo dakin tare da Dr din da yayi discharging Mayraah, Dr din na kallonta murmushi kwance fuskarsa yace "I can see you are feeling much better now" Ta sunkuyar da kanta yace "Sauran injections dinki Dr Maheer zai dinga maki a gida ya ci gaba da baki duk kulawan da ya kamata" Dr Musharraf ya daga kai ya kalli Maheer suka hada ido, shi ya fara dauke idonsa, likitan ya ci gaba yace "Sannan ki cire duk wani abinda ya dameki a zuciya ba a san musulmi da haka ba kin ji, idan kina da damuwa ne u have ur brother's that care soo much about you, ki gaya masu duk wani damuwarki they will always be there for u from they way naga sun damu da lamarin ki..." Dr Musharraf ya juya ya fita daga ward din, Mayraah ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, likitan dai ya gama bata shawarwarin da ya kamata amma fa duk bata san abinda yake cewa ba tunda dai Musharraf ya fita, likitan ya kalli Maheer daga karshe yace "To ango, za ku iya tafiya da kanwarka... That's all i have to say to her, Allah Ubangiji ya tsare gaba, ya kara mata lafiya, kai kuma Allah ya baka zaman lafiya da amarya" Maheer yayi masa godiya sosai, likitan ya bar ward din, Maheer na kallon Mayraah dake kokarin sauka daga saman gadon ya karasa ya mika mata hannu da nufin taimaka mata ta sauka, ta dauke kai taki basa nata hannun har ta sauka, a hankali take tafiya don sai taji jikinta babu kwari, and she is still feeling a bit dizzy, yana biye da ita a baya suka fita daga ward din, tun da suka fito haraban asibitin take bin ko ina da kallo amma bata ga alamar motar Dr Musharraf ba balle shi, shi kansa Maheer shi yake ta dubawa da ido a compound din amma sai yaga motarsa ma bata nan hakan ya tabbatar masa ya tafi, Maheer dai bai ce komai ba har suka iso gun motarsa ya bude mata back seat yana kallonta, ta sunkuyar da kanta ta shiga ya kulle, lokaci daya hawaye ya cika idonta ta jinginar da kanta jikin kujeran motar, ya zaga ya shiga front seat ya tada motar suka bar asibitin, sai da suka hau saman titi yayi dialing number Musharraf, sai da ya kusa katsewa Musharraf ya daga, Maheer yace "Ka tafi ne Dr? I can't find ur car at the space provided for parking" Dr Musharraf yace "Yea, i received an urgent call shi yasa na tafi" Maheer yace "Ohk, muna hanya za mu tafi gida yanzu in sha Allah" Dr Musharraf yace "To Maa sha Allah, Allah ya tsare" Maheer yace "Ameen" Daga haka ya katse wayar, Mayraah dake sauraron conversation din nasu jikinta yayi sanyi sosai hawaye ya kasa daina zuba idonta, all through the ride babu wanda yace komai cikin su, kowa da tunanin da yake a ransa, sai da Mayraah taga sun shigo layinsu ta hade kai da gwiwa hawaye masu zafi na sauka idonta, yanzu kenan kowa a anguwan nan yasan wacece ita? Everybody now knows she is not the daughter of her supposed parent, kowa yanzu yasan ita bata da asali kenan, tunanin nan yasa ta fara jin numfashinta na sama, har Maheer yayi parking a compound bata san yayi ba, ya zaga ya bude back seat yana kallonta cikin sanyin murya yace "We are home Mimi" Ta dago kanta da kyar, ganin yanda take numfashi ya kamo hannunta da sauri yace "Are you okay?" Bai jira me zata ce ba ya sauko da ita daga motar yana kallonga da damuwa yace "Me yasa kike haka Mimi, kina son ki daura ma kanki wani ciwon ne? Why are you doing this to us pls?" Ya jinginar da ita jikin motar har ya ga numfashin ya fara dawo mata dai dai, ya hade rai yace "Why are you doing this plss Mimi?" Ta sunkuyar da kanta tana sauke numfashi a hankali, ya kama hannunta ya nufi visitors part saboda mutane na gidan har sannan kasancewar za a kawo Haseenah zuwa bayan Magrib tunda dai an daura aure babu abinda ya rage, Babu kowa babban parlon Maheer ya karasa cikin Bedroom din dake cikin parlon yana rike da hannunta, ya zaunar da ita gefen gado ya durkusa gabanta cike da damuwa yace "Don Allah Mimi ki cire duk wani abu da kika sa a ranki yake damunki, we all felt what u feel today, kamar yanda aka boye maki wannan abun mu ma haka aka boye mana, duk kusanci na da Abba bai taɓa gaya min wannan maganar ba, kuma so ne yasa suka mana haka Mimi, don Allah kiyi hakuri mu yi accepting fate din nan da hannu bibbiyu mu gode Allah, but keep in mind nothing can change the fact cewar ke jininmu ce har gobe har abada, you still remain our lil sis" Shiru tayi tana kallonsa hawaye masu zafi na sauka idonta, yayi kasa da murya yace "Say Alhamdulillah Mimi" Ta sauke idonta a hankali tace "Alhamdulillah" Maheer ya mike yace "Let me get u ur hijab kiyi sallah" Daga haka ya juya ya fita daga dakin, ta zamo kasa tana son ganin bata fashe da kukan da ya taho mata ba amma ta kasa, kuka take kamar ranta zai fita abubuwa iri iri na yawo a kanta, yanzu kilan da tun farko tasan fate dinta kowa yasan wacece ita da ba a fasa aurenta da Musharraf ba, amma saboda su Abba sun boye asalin wacece ita shi yasa duk abun nan suka faru, jin an bude kofar dakin ta daga kai tana kallon kofar, Usman ya shigo rike da Hijab dinta, suna hada ido ta sunkuyar da kai, ya karasa har inda take, after standing for like 20 seconds, ya duka gabanta ya ajiye mata hijab din yana kallonta, ita dai har sannan bata daga kanta ba, yayi kasa da murya yace "You say Alhamdulillah in all situation.... And that is among the etiquette of being a devoted muslim, but get this straight..., nothing can alter the fact of u being our sibling, we love u and will continue loving u the way we do forever, Ammi and Abba remains ur parent now and forever" Mayraah ta daga kai tana kallonsa, ya sa hannu ya goge mata hawayen idonta ya sakar mata murmushi yace "That's it, we love you no matter what" Ta sauke idonta kasa, yace "Ki shiga toilet kiyi alwala, it's almost Magrib, i will be going to mosque too" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, tun farkawanta a asibiti sai yanzu tayi feeling a bit relieved daga damuwar da suka yi layi a zuciyarta, a hankali ta mike ta fito parlor ta shiga bandakin dake ciki don yin alwala. Mayraah ta idar da margrib bayan duk ta rama sallolin dake kanta tana linke darduman da tayi sallan Aunty Mariya ta shigo parlon, duk bata san Mayraah na gidan ba sai yanzu da Maheer ya sanar mata bayan ya dawo daga masallaci, dama Usman kawai ya gaya ma tun dawowarsu, Mayraah ta sunkuyar da kanta ganin Aunty Mariya, Aunty Mariya ta nufeta ta rungumeta cike da farin ciki tace "Welcome back home daughter, Maheer bai gaya min kun dawo ba sai yanzu, hope you are feeling much better now?" Mayraah ta gyada mata kai, Aunty Mariya tace "Toh Alhamdulillah, mun gode ma Allah, naga heater din bandakin nan baya yi bari in kawo maki ruwan zafi kiyi wanka ki canza kaya, ki ci abinci yanzu" Mayraah dake kallonta a hankali tace "Aunty, Ammi fa" Aunty Mariya tayi murmushi tace "Kina wanka in kin ci abinci zaki je ki dubata, yanzu bacci take" Aunty Mariya ta zaunar da ita kan kujera tace "Let me get you the hot water dear" Daga haka ta fita daga parlon, dai dai nan yan kawo Haseenah suka iso gidan a motoci biyu, da yake family din nata masu hankali ne sun san abinda ke faruwa ba a wani yi zugan kawota ba, don bai fi mutum bakwai bane suka taho da ita.... Aunty Mariya bata tsaya an amshi Haseenah da ita ba don duk hankalinta na kan Mayraah, tuni ta kai mata ruwan zafi bangaren visitors, ta surka mata ruwan da kanta a bandaki, dama ta taho mata da sosonta da shower gel da towel, bata bari kowa yasan Mayraah na gidan ba, bayan Mayraah ta shiga wanka ta sake komawa cikin gida ta dauko mata kayan sawanta da kayan shafe shafe, nan parlon ta ajiye mata don ta gani idan ta fito daga bandaki sannan ta sake komawa cikin gida hado mata abinci da shayi, she is so happy yanayin da ta ga Mayraah kamar ba ita dazu ba.. Mayraah ta fito parlon daure da towel tana kallon kayan da Aunty Mariya ta ajiye mata kan kujera da turarrukanta at the same time tana tunanin inda zata samu waya ta kira Dr Musharraf, bude kofar parlon aka yi ta juya taga Usman, lkci daya ya juya ya bi gefen Maheer dake bayansa shi bai kai ga shigowa parlon ba, Maheer ya bi sa da kallo ganin ya fito, bai dai ce masa komai ba ya shiga parlon shi ma, Tuni dama ta durkusa kasa tana zare ido, Maheer yace "Ohh sorry, finish wearing ur clothe" daga haka ya juya ya fita, ta kwashe kayan ta shige daki da sauri.
Haseenah na zaune dakin da Hajja da Mama Ladi suke an shigo da ita ta gaishesu Aunties dinta uku na zaune gefenta, Hajja dai ta sa mata albarka sannan tayi mata nasiha irin ta manya a takaice, daga karshe tana murmushi tace "Allah kuma ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Allah ya sa gidan zamanki ne na har abada, Allah ya albarkaci auren...." duk yan dakin suka amsa da "Ameeen ya Allah" Mama Ladi ta ajiye kwanon tuwon da take ci tace "Sai dai kuma anyi biki duk bama cikin kwanciyar hankali muna cike da alhinin abinda ya same mu, don da an biye ta Mashir ma ɗaga bikin nan za ayi sai xuwa duk sanda Allah ya nufa, don bakina da nasa yace min lafiyar kanwarsa ta fiye masa wannan auren shi, ta yaya zai yi aure kanwarsa na gadon asibiti, mu dai muka ce ya rufa mana asiri kar ya maida mu kananun mutane a idon duniya ayi ta yamadidi da mu, magana ta zama biyu a kanmu, ga na Mera ga na Mashir" Sake baki Hajja tayi tana kallonta cike da takaici, ba Hajja kadai ba duk yan uwan Ammi da suke dakin haka suka sake baki suna kallon Mama Ladi cike da mamaki, Haseenah ma ta dinga lekota ta cikin mayafi tana jin zuciyarta na bugawa don ita kanta ai ya gaya mata makamancin haka a waya, wato ashe da gaske ma yake??? Mama Ladi ta dau ƙashin dake kwanon abincinta tana gwagwiya tace "Mu kanmu tun safe bamu gansa ba yana can asibiti da Mera, ko er farar shaddan biki da angwaye ke sa wa ma ban ga ya sa ba duk yau, yana ta yawo da wata jallabiya ruwan hoda ko guga babu sai daga baya nake samun labarin ko wajen daurin auren ma bai je ba, Yo banda uban nasa ma yace a taho dake yau a in don ta shine tarewarki ba yanzu ba sai sanda Mera ta farfado kin ga kuma ba rana kenan, ai yau kam mun ga jarabawa ganin idonmu, don haka nake baki shawara ki zama me kwantar ma mijinki da hankali akan wannan iftila'i da ya fada mana, ai kinsan an fasa auren Meran ko? To in gaya maki dazu matsiyatan dangin shegen da zata aura suka zo kwashe kayansu da suka kawo nan, da jefe jefe muka rabu da yan iska, nayi masu wankin soso da sabulu nace masu gayyar tsiya" Maman Shafa na kallon Aunties din Haseenah tace "Kamar baku je bangaren Ammi ba ko? Muje in kai ku nasan yanzu ta farka tunda anyi magariba" Tana fadin haka ta mike, Aunties din Haseenah da sai kallon Mama Ladi suke, har dai suka daga Haseenah suka bar dakin, Mama Ladi ta bi Maman Shafa da harara ta ajiye ƙashin hannunta cikin kwano tace "Wai ita kuma wannan katuwar dake yawo da kodadden zani da yagunannen hijabi wacece ita fisabilillahi? Naga sai shigar min hanci take da kudundune tun da garin Allah ya waye, banda taron biki me zai hadani waje daya da ita mata kamar almajira kaya duk a yamutse" Rai bace Hajja tace "Ladi ke yanzu baza ki saka ma bakinki linzami ba, wllh kar ki bari in maki koran kare daga gidan nan, kin isheni kuma haka tsakani da Allah, wannan wani irin bala'i ne baki gyara abu sai dai ki tabarbare lamari" Mama Ladi tace "Wai kiyi ta cewa zaki min koran kare yaya, ni fa gidan Mamuda nake ba gidan kowa ba, daga magana sai a juya min a fassara abinda nake nufi ta wata tsigar? Ko don anga ban haihu ba balle in aurar da jika?" Tana fadin haka ta fashe da kuka ta jawo mayafinta tana matsar kwalla ta mike ta fice daga dakin da kwanon abincinta. Mayraah na biye da Aunty Mariya suka shigo parlon Ammi, babu wanda ya lura da shigowarsu gidan don ta baya suka shigo ta bangaren Abba, Ammi na zaune kan darduma bayan Hajiya Safiyya ta cire mata drip din hannunta tayi sallah har ta idar, ta daga kai tana kallon Mayraah babu ko kiftawa don bata ma san sun dawo gida ba, nan da nan Mayraah taji hankalinta ya tashi don daga fuska zaka fahimci Ammi na jin jiki, ta karasa da sauri ta durkusa gabanta ta riko hannunta tace "Ammi are you this sick??" Ammi ta rungumota jikinta amma ta kasa cewa komai, kuka kawai Mayraah take a jikinta, Ammi ita ma hawaye ne ke sauka idonta, Babu wanda yace masu komai a dakin, cause bond din exactly irin na uwa da ɗan ta, Aunty Mariya dai na tsaye bakin kofa ta ma kasa karasowa cikin parlon duk jikinta yayi sanyi, Kwankwasa kofar parlon aka yi, Maman Shafa ta leko tace "Za a shigo da amarya wajen Ammi" Aunty Mariya tace "Ohk to ana zuwa" Aunty Mariya ta nufi Ammi da damuwa tace "Plss kiyi composing din kanki Ammi, za a shigo da Haseenah" Aunty Mariya na fadin haka zata janye Mayraah daga kusa da Ammi a hankali Ammi tace "Ki bar ta, su shigo kawai ba komai" Aunty Mariya da Hajiya Safiyya suka yi mamaki sosai don fa tun safe Ammi bata yi ma kowa magana sai dai ta bi ka da ido kawai, Aunty Mariya ta koma tayi masu iso har cikin parlon don dama an shimfida tsadadden carpet babba, Haseenah da Aunties dinta suka zauna, Mayraah dake makale jikin Ammi ta daga kai tana kallonsu, cike da karfin hali Ammi ke amsa gaisuwarsu da ya jikin da suke mata, Haseenah kuwa sai leko Mayraah take ta cikin gyale don sarai ta ganeta, nan taji bacin ranta ya ninku, wato saboda wannan er iskar aka yi bikinta kamar ana zaman makoki yau ko? Frnd din Ammi ce tayi ma Haseenah nasiha wanda Ammi zata yi mata, amma duk Haseenah bata san me take cewa ba don gaba daya hankalinta na kan Mayraah da tunani iri iri da take yi a kanta....
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788.... In kinsan baki biya for subscription na littafin nan ba kiji tsoron Allah ki zo ki sallami jikar inna marainiya.