Page 14
Maheer na zaune kan kujeran dake kusa da gadon dake dakin asibitin ya jinginar da kansa da kujeran idonsa a lumshe, Usman na tsaye jikin window din dakin yana danna wayarsa, lkci lkci yake daga kai ya kalli saman patient bed din da Mayraah ke kwance, she is being unconscious tun safe sai wajen karfe daya da wani abu ta farka, tana farkawa kuma babu bata lokaci aka mata wani allura shine har yanzu take bacci and this is almost 4pm, motsi yaga tana yi, ya saka wayarsa a aljihu ya nufeta, ya duka a bit closer to her yana kallonta, bude ido tayi a hankali, tana hada ido da shi ta fara kokarin tashi zaune, Usman ya rike hannunta yace "Do not injure ur self, akwai drip a hannunki" Bude ido Maheer yayi da sauri, lkci daya ya mike tsaye holding on to her yace "Are you okay Lil sis?" Mayraah dai sai kalle kallen dakin asibitin take, Maheer ya fahimci she is trying to recall things, ya maidata ta kwanta yace "Lay still, you will be fine in sha Allah Mimi" Bin su Mayraah ta shiga yi da kallo kamar ranan ta fara ganinsu, bayan kanta da yayi mata nauyi har kirjinta ma ji tayi yana mata wani azababben ciwo, dafe kirjin tayi tana son magana amma ta kasa, Maheer dake rike da ita har sannan yace "Kina jin ciwo a nan ne?" Kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta, yasan dole zata ji haka cause she had a terrible panic attack that triggered her Asthma, tun daga gida yayi kokarin reviving dinta har suka taho asibitin aka kwantar da ita giving her the necessary treatment, ya jinginar da pillow din kan gadon da bango sannan ya sa tayi resting a jiki yace "U will feel relieved in sha Allah" Usman ya koma inda yake ya tsaya yana kallonsu, Maheer ya bude flask din da Aunty Mariya ta kawo masu da kayan shayi don ko minti talatin bata yi da barin asibitin ba, yayi making din mata shayi ɗan kadan a cup yayi diluting da bottle water sannan ya mika mata a hankali yace "Ki daure ki sha ko kadan ne sai a maki allura for the chest ache" Bata ce masa komai ba don tayi nisa tunanin da ta tafi, ya zauna gefen gadon yana kallonta, sai da yayi gathering courage kafin a hankali yace "Mimi" ta dawo duniyar tunanin da ta tafi tana kallonsa, yace "Amshi shayin ki sha even if it's just a little" Sauke idonta tayi kasa without responding to him, wayarsa ne ya fara ring a aljihunsa ya ciro ganin Abba ne ke kiransa ya daga ya kai kunne, ya gyada kai yace "Eh ta tashi" Yana fadin haka ya kalli Mayraah yana mika mata wayar yace "Za ki yi magana da Abba" Girgiza masa kai kawai tayi ba tare da ta kallesa ba, ya maida wayar kunnensa a hankali yace "Zan kira ka Abba" Ajiye wayar yayi bayan Abba ya katse yana kallonta, ko bata ce komai ba kasan she is in pain, ya ajiye cup din shayin ya juya ya fita daga ward din don kiran likitan da ya amsheta to make some suggestions on more injections da za ayi mata ko zata samu relief gaba daya, Shi dai Usman na tsaye ya rungume hannayensa yana ta kallonta, ta daga kai ta kallesa suka hada ido, sai kuma ta sunkuyar da kanta hawayen dake makale idonta ya sakko fuskarta, jinginar da kai yayi da bango not knowing what to even say to her, he wish he could take away her pain and grief, Maheer na dawowa tare da likitan wayarsa ya fara ring ya ciro a aljihunsa ya ga Haseenah ce, ta kirasa yafi sau arba'in yau, tun da garin Allah ya waye take kira ko daya bai daga ba a kiran sai ma silencing din wayar da yayi ya bar sa a aljihu, ya bar likitan ya shiga ward din shi kuma ya tsaya daga corridor yayi picking din call din nata, babu ko sallama a fusace ta fara cewa "Yanzu Maheer fisabilillahi yau daurin auren namu guda tun da garin Allah ya waye ko message dinka ban gani a wayata ba balle kiranka? Sannan ban yi fushi ba ni ina ta kiranka amma still ka ki daga min waya alhalin nasan kana gani ba wai baka gani ba? Ko wace amarya ana daura aure angonta ke kiranta yayi mata albishir sannan yayi masu fatan zaman lafiya amma kai babu kira babu message sannan na samu labarin ko daurin auren baka je ba wajen cousins dina, Maheer ko ka mance yau ranar ka ce? Ka mance sau daya ko wani mutum a duniya yake experiencing wannan babban ranan?" Maheer dake ta sauraronta yace "Are you trying to tell me baki san kanwata na kwance unconscious a hospital ba all through today?" Haseenah ta wani hade rai tace "To waye zai gaya min tunda ni dai ba bokanya ba? Kuma ba a gidanku nake ba, how will i know??" Maheer yace "To banda Abba da yayi insisting a daura auren nan yau ban yi niyyar a daura auren ba, because bani da wannan nutsuwar seeing my sister on sick bed....." Haseenah ta zaro ido zuciyarta na tafarfasa tace "Ohh saboda kanwarka bata da lafiya shine ka so cewa a daga daurin auren mu yau Maheer?" Maheer yace "Ke malama kar ki wuce limit dinki, banda ni me biyayya ne ga mahaifina da baza a daura auren nan yau ba am telling you the fact, ta yaya za a daura min aure with my sister unconscious on bed?? If not for my father i don't think that would be possible" Haseenah was shock, don tsabar shock kasa ce masa komai tayi ta ji ya katse wayarsa... Shiga ward din yayi, likitan ya juya yana kallonsa yace "Dr za a shigo ayi mata wasu alluran yanzu, so pls let her take a little thing" Maheer yace "Toh mun gode Dr" Karasawa yayi kusa da ita ya dau shayin yana kallonta cikin kwantar da murya yace "Pls ki sha ko kadan ne Mimi" Girgiza masa kai tayi hawaye na taruwa idonta har sannan bata bude baki tayi magana ba, ya ciro handkerchief dinsa yana goge mata hawayen yace "Don Allah ki sha kin ji" Shi dai Usman na tsaye yana kallonsu, Maheer ya ciro wayarsa dake ringing, ganin me kiransa ya daga ya kai kunne, description din zuwa ward din da suke yayi a wayar sannan ya katse, yana ci gaba da lallabata ta sha shayin, amma taki ko amsa balle ta sha, sai lallabata yake ta sha, bayan few minutes aka bude kofar ward din, duk suka daga kai suna kallon kofar, Mayraah ta dinga kallonsa har ya karaso ciki, gun Usman ya nufa ya basa hannu yana kallonsa suka gaisa, Maheer ya mike daga gefen gadon da yake zaune, ya basa hannu suka gaisa yace "Ya me jiki?" Maheer yace "Alhamdulillah" Mayraah dai har sannan kallonsa take, Ya karasa kusa da gadon a hankali yace "Ya jikin?" Wasu sabbin hawayen suka cika idonta, bai san sanda ya dafa gadon ba murya can kasa yace "No plss, stay strong Mayraah, everything will be alright in sha Allah" Ta sunkuyar da kanta hawayen bai fasa zuba idonta ba, ji yayi kamar ya jawota jikinsa ya lallasheta yanda ya kamata don kukanta karyar masa da zuciya yake tun ba yanzu ba, Wata Nurse ta shigo ward din bayan ta kwankwasa kofar, tana kallon Maheer tace "Ta sha tea din?" Maheer yace "Not yet amma yanzu zata sha" Nurse din tace "Ohk za a mata allura ne i will come back in some minutes time" Tana fadin haka ta juya ta fita, Dr Musharraf ya kalli shayin dake ajiye gefensa a cup, ya dauka ya mika mata yace "Ki sha kadan za ayi maki allura" Ta daga kai ta kallesa, ba musu ta amsa ta kai bakinta a hankali, Maheer felt much relieved da ya ga ta amshi shayin, ya juya ya fita daga ward din don an fara kiran Asr, Juyawa Usman yayi shi ma ya fita, Mayraah ta bi su da kallo, bata san sanda ta ajiye cup din ba ta fashe da kuka, nan da nan hankalin Musharraf ya tashi yace "Plss ki daina kukan nan haka Mayraah, u had a panic attack..." Cikin rawan murya tana kallonsa tace "But where can i get my parent?" Musharraf da jikinsa yayi sanyi sosai yayi shiru yana kallonta, can ya zauna gefenta a hankali yace "Do not be an ingrate Mayraah, har a yanzu Abba da Ammi are your parent, and they will keep on being a parent figure to you" Sosai take kuka cike da rauni tana kallonsa, zuciyarsa ya karaya ya ma rasa abinda zai ce mata, ya jinginar da kansa da bango ya lumshe ido yana wishing he could take all her pains away, Nurse din ce ta dawo ward din rike da alluran da zata ma Mayraah tace "Hope ta sha shayin?" Musharraf ya mike ya dau cup din shayin ya kai mata baki yace "Pls take even if it's little za ayi maki allura" Ba musu ta amshi cup din a hannunsa ta fara kurban shayin da kyar, ya dinga encouraging dinta tana shan shayin har ta kusa shanyewa, daga karshe ta ajiye masa cup din tana girgiza kai tace "Zan iya yin amai" Ya dau sauran shayin ya ajiye kan overbed table dake kusa da gadon, sannan ya kalli nurse din da ta karaso kusa da Mayraah, juyawa yayi ya nufi kofa zai fita, a hankali yaji tace "Baza ka tafi ba ko?" Ya juya yana kallonta kamar yanda take kallonsa ita ma, yace "I will wait outside ta maki alluran" Mayraah ta gyada masa kai, ya fita ya kullo masu kofar ward din, nurse din na gama mata alluran bayan ta fita Musharraf ya koma dakin, hawaye ya gani idonta, da mamaki yace "Injection din kike ma kuka?" Ita dai bata kallesa ba kuma bata ce masa komai ba, ya dinga kallonta, kamar wanda ya tuna wani abu ya juya da sauri yace "An tada sallah, let me go to the mosque" a hankali tace "Will u come back?" Yayi shiru yana kallonta, can yace "Are you afraid of anything?" Ta girgiza masa kai tana share hawayen da yaki tsaya mata cikin sanyin murya tace "I am no longer comfortable" Shiru yayi bayan bayan few seconds yace "Am not leaving you" Daga haka ya juya ya fita, Ta koma ta kwanta maganganun Mama Ladi na mata yawo a kwakwalwarta kamar a lokacin take fadan su, Mayraah bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba tana jin zuciyarta na mata zafi sosai, bata san for how long she have been crying ba taji an bude kofar ward din, ta kulle idonta da sauri, muryar Maheer taji kusa da ita a hankali yace "Mimi" Still taki bude idon kai sai kace bacci take, Maheer ya ajiye fruits din da ya siyo mata outside of the hospital a kan overbed table sannan ya zauna kan Plastic chair yana kallonta don a tunaninsa bacci take, bayan some minutes Usman ya shigo ward din, yana kallon Maheer yace "I will be going home now to check on Ammi" Maheer yace "Ohk..." Daga haka ya fita daga ward din, Maheer ya ciro wayarsa dake vibrate, Tun yana sallah Haseenah ke kiransa, yaga calls goma tayi masa a mintunan da basu wuce 15 ba, ya daga kiran ya kai kunne, babu ko sallama tace "Maheer wai me kake nufi da dinner dinmu ne yau? Naga har anyi la'asar banji kace min ga abokanka nan zuwa da motoci ba" Maheer rasa abinda zai ce mata ma yayi tsabar takaici, Haseenah tace "Hello" Calmly yace "Ina jin ki" Tace "Ohh da kana ji na kayi shiru, wai ko ka manta munce babu African time ne? Nan da awa daya da wani abu fa ya ci ace duk muna can" Yace "Haseenah" Tace "Ina jin ka" yace "Kije ke da kawayenki da yan uwanki ku yi dinner din, i, my relatives, and my frnds won't be available" Haseenah ta wani zaro ido tace "What?? Ban gane me kake nufi ba Maheer" Yace "Abinda kika ji na fada shi nake nufi tunda ba wani yaren daban na yi maki ba, beside nasan Mumy da sisters dinta baza su rasa gaya maki halin da Mimi take ciki ba tunda sun zo duba ta wajen karfe daya ai" a fusace Haseenah tace "Wannan kai ta shafa Maheer don ni babu abinda ya sha min kai, kuma akan wata can bazan ɓata wannan day din nawa ba wallahi, abu dai da sau daya zanyi witnessing dinsa a duk rayuwata shine za ayi min haka? Naga dai ai ba kai kadai bane a gidan da dole sai kai zaka tsaya da ita a asibiti, don me ma wata tsohuwa a danginku bazata zauna da ita a asibitin ta kula da ita ba sai kai?" Maheer dake ta sauraronta yace "Mayraah din kike ce ma wata?" Ta fashe da kuka tace "Nace din Maheer, abinda duk labari ya gama bazuwa a duniya ashe babu abinda ku ka hada da ita er tsintuwa ce ba Ammi da Abba suka haifeta ba..." Maheer ya mike yace "You've successfully cross ur boundary Haseenah, wllh wllh kika sake furta wani kalma akan Mayraah a yau din nan zan datse igiyarki dake kaina, yanzun nan zan datse alaqar da aka kulla mana just some hours ago without second thought and no regrets" Haseenah that was soo shock and speechless ta buda baki tana sauraron abinda yake gaya mata a kunne, yace "Nonsense" Daga haka ya katse wayar, duk wannan abun Mayraah na jin su hawaye kawai ke sauka idonta. Bude kofar ward din aka yi Aunty Mariya ta shigo rike da basket me dauke da abinci a ciki, Maheer da har sannan xuciyarsa ke tafarfasa akan abinda Haseenah ta fada masa kan Mayraah ya nufeta ya amshi abincin hannunta yace "Sannu da zuwa" Aunty Mariya dake kallon Mayraah a sanyaye tace "Ta farka kuwa?" Maheer yace "Ta farka dazu, amma yanzu bacci take an mata allurai ne" Aunty Mariya ta zauna kan kujera duk abun duniya ya taru ya mata yawa ga Ammi ana tunanin za a taho da ita asibiti a kwantar da ita don jikin nata sai a hankali har yanzu, dafe kanta tayi a hankali tace "Sun je sun kwashe kayansu, in gaya maka abun ba mutunci Maheer, ban taɓa ganin matsiyata mara su kirki ma irin mutanen nan ba, sai kaga abinda suka mana wllh, don ma bakin Mama Ladi da wata makociyarku Maman Shafa bakinsu ba shiru yayi ba, abinda suka manta ne kawai su ma basu gaya masu ba, duk da su suka fara sakin maganganu, Mama Ladi ta fara dura masu zagi, abun dai ba dadi kai dai in gaya maka, zuga guda fa suka yo kamar yaƙi wai sun zo kwashe kaya, Allah ya rufa mana asiri an ga Gwal din nan da ban san ya za a kaya yau ba, don ba lallai ma su hakura muje kasuwa mu nemo ba tara mana jama'ar anguwa kawai za su yi, amma anya da amincewar iyayensa yaron nan ya nemi Mayraah kuwa Maheer? Alamu duk sun nuna dama tun farko they were not in support of the marriage kafin wannan abun ma ya billo" Maheer dai yayi shiru yana kallonta don ya ma rasa abinda zai ce, Aunty Mariya na girgiza kai cike da takaici tace "In the other way round ni sai naga kamar rashin auren ma shi yafi alkhairi da dai wannan tashin hankalin da na gani da idanuwana yau..." Bude kofa aka yi Musharraf ya shigo ward din, Maheer ya sauke kansa kasa codedly yace "Do not say anything, shi ne" Aunty Mariya ta juya tana kallon Musharraf don bata san sa ba, ya karaso ciki ya gaisheta da ladabi, a dakile ta amsa ta dauke kai, Musharraf ya ajiye ledan fruits din hannunsa, Maheer na kallonsa ya ɗan yi murmushi yace "Nima na siyo mata, amma naga bacci take" Musharraf yace "Ohk" duk wannan abun Mayraah na jin su kawai ta rufe ido ne kamar tana bacci, amma ita kadai tasan abinda take ji a duk jikinta most especially her chest and her head that is banging, Musharraf ya juya ya nufi kofa cause duk sai jikinsa yayi sanyi ganin yanda Aunty Mariya ta amsa masa gaisuwa ta dauke kai, Maheer yace "Amma ba tafiya zaka yi ba" Mayraah bata san sanda ta bude idonta da sauri ba jin abinda Maheer yace, amma ta daure bata bari ta juya ba balle su gane idonta biyu, banda bugawa babu abinda zuciyarta ya fara yi da sauri da sauri, Musharraf ya ɗan yi murmushi yace "Aa ina waje" Maheer yace "Ohk" Daga haka Musharraf ya fita ya kullo masu kofar, a fusace Aunty Mariya tace "To uban me ya biyota nan yayi mata kuma? Yau naga iskanci" Maheer ya kwantar da murya yace "Aunty shi fa bashi da laifi, dangin Abbansa ne suke ta wannan abun, ba shi ne yace bazai aureta ba, fin karfinsa aka yi a gida, kuma kinga ba shi da yanda zai yi tunda ga abinda iyayensa suka ce" Aunty Mariya ta wani ja tsaki tace "To me zuwansa nan zai kara mana da shi? Gwara kawai yayi tafiyarsa ni bana son ganinsa gaskiya, yayi tafiyarsa kawai ba a bukatansa ya bar mana er mu ta dawo hayyacinta cikin aminci, tun ban bude baki nayi masa magana ba ka sallamesa gaskiya" Maheer dai ya ma rasa abinda zai ce mata ganin yanda ta hasala, Ta ci gaba tace "Wannan ai rashin kunya ne ma, salon ta farka tayi arba da shi abu ya kara lalacewa" Maheer dake neman yanda zai kauda zancen yace "Aunty Hajja fa?" Aunty Mariya tace "Tun dazu in gaya maka ta daga hankali ita zata tafi Bichi banda hanata da aka yi, kasan Badiyyar ta gudu ta tafi can ai, to shine wai take son zuwa ta sanar ma dangin ubanta abinda ta aikata, mun dai hanata don yanzu ba wannan bane a gabanmu, yanda Mayraah zata dawo hayyacinta ta kwantar da hankalinta, ita ma Ammi Allah ya bata lafiya is our major concern now" Maheer ya girgiza kai a ransa yana tunanin abinda zai yi ma Badiyya da za su yi ido hudu da ita, Aunty Mariya ta mike tace "Bari in koma gida wajen Ammi Maheer, in dai ta farka don Allah ka kirani, Hajja ma na son a kawota nace ta bari sai ta farka, karya muka masu ba a barin kowa ya shiga inda take shine muka samu lafiya amma da jama'ar da za su cika asibitin nan ai sai Allah yau" Maheer bai ce komai ba ya rakata suka fita, Aunty Mariya na kallonsa tace "Abba ya zo?" Maheer ya girgiza kai yace "Tun dai wajen karfe biyu da ya tafi" Aunty Mariya bata kuma cewa komai ba har suka fito haraban asibitin, zaune suka tadda Musharraf a karkashin bishiya, Ya mike yace "Allah ya tsare Aunty" Aunty Mariya tayi kamar bata ji sa ba ta shige mota tayi wucewarta, Maheer sai duk bai ji dadi ba, ya nufi Musharraf yace "Let me make some calls, ka ɗan shiga ciki ba kowa" Musharraf yace "Ohk" Maheer ya zauna karkashin bishiyar, Musharraf ya nufi cikin asibitin, Maheer yayi haka ne don yana tunanin ko da ta farka idan ya bata abincin zata ci tunda dazu da ya bata shayi ta amsa a gun sa.... Musharraf na shigowa ward din Mayraah ta juya jin kamshin turarensa, ya karasa kusa da gadon yana kallon drip din da sai a sannan yayi rabi, yayi kasa da murya yace "Are you still feeling much pain in ur chest?" Ta girgiza masa kai, don tun da aka mata alluran taji ya ɗan mata sauki ba kamar dazu ba, ya ɗan kara gudun ruwan, sannan ya bude basket din da Aunty Mariya ta kawo ya bude warmer din abincin, irish porridge ne da yaji hanta sai kamshi yake, Duk da halin da Ammi take ciki hakan bai sa ta mance abincin da Mayraah ke iya ci in dai bata da lafiya ba, haka ta sa Aunty Mariya tayi mata sannan aka mata pepper soup din ƙoda, Mayraah dai sai kallon Musharraf take, ya dau plate ya debar mata abincin ya sa cokali a ciki sannan ya mika mata yana kallonta yace "Plsss ki daure ki ci ko kadan ne" Hawaye ya cika idonta sai a yanzu maganganun da yayi mata ranan da taje kai masa abinci da magani suka dinga dawo mata, she now understands why he said in dai shi bai bar ta ba bata da wani hujjan barin sa, wato tun ba yanzu ba yasan da wannan maganar shine yaki gaya mata, bata san sanda ta fashe da kuka ba ta hade kanta da pillow, Musharraf ya ajiye plate din hannunsa kan overbed table da sauri yace "Are you okay?" Ta dago tana kuka sosai tana kallonsa tace "Why did my parent abandon me? Where can i find them?" Musharraf yace "No Mayraah, don't be an ingrate like i said before, butulci zaki ma su Ammi da Abba? What is it that u lack from them as parents? Love? Care? Or what? Meye basu maki ba a cikin wanda iyaye ke ma 'ya yansu?" Cikin kuka tace "But i need to know my real parent, bazan iya ci gaba da kallon su Yaya Maheer as people that i am not related with ba, i can neva be comfortable any longer, all this years me yasa aka...." Kasa ci gaba tayi ta dinga kuka, Musharraf da duk jikinsa yayi sanyi ya dinga kallonta because he understands her feelings, yanzu jin ta zata dinga yi kamar bare a cikinsu, nothing will ever change that a zuciyarta, kamar fa yanzu ne ace masa ba Mami bace ta haifesa he can't even imagine that, ba ma shi ba, koma waye won't like to imagine that balle har ya faru a kansa, the shock, confusion and disappoinment kadai ya isa ya jefa mutum into depression, ta dafa hannunsa tana kuka sosai amma ta kasa maganar da take son yi masa, nan da nan ta sa idanuwansa suka kada yana jin kukanta har cikin ransa, yayi wrapping hannunsa cikin nata a hankali yace "I will neva let you down Mayraah, ki amince da ni mu je a daura mana aure somewhere else, i will give you all the love and care u deserve in this world, kuma na maki alkawarin i can use my last breathe wajen ganin kin hadu da iyayenki na asali" Ita dai ta kasa cewa komai kuka kawai take, Yace "Kin amince za ki bi ni?" Ta girgiza masa kai da kyar tace "Danginka basu so na even before finding out who i am, za su iya disowning dinka...." Katse ta yayi a fusace yace "For all i care, as far as ba Mami bace zata yi disowning dina, Mayraah a shirye nake da ko wani challenges da zan fuskanta saboda ke a rayuwar nan" Ta goge idonta tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Sai mu je ina?" Yace "Idan an daura mana auren we will sort that out" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, Musharraf yayi kasa da murya yace "Idan Maheer ya shigo u should let him know that u need ur Hijab, nasan zai ce zai je gida ya dauko maki kafin ya dawo i will find a way da za mu bar asibitin nan" Ko rufe baki bai yi ba aka bude kofar ward din, suka sake hannun juna da sauri, ya mike tsaye ya dau plate din porridge din yana mika mata, ta amsa, Maheer ya shigo ward din, ko minti biyu bai yi da shigowa ba Musharraf yace "Let me get something outside" Maheer yace "Ohk" Daga haka Musharraf ya fita daga dakin, Maheer ya karasa kusa da Mayraah dake ta juya abincin hannunta da spoon, she became so uncomfortable da ya dawo kusa da ita, ta ki yarda ta kallesa kamar wani stranger haka take jin sa, a hankali yace "Mimi" Ba tare da ta kallesa ba bakinta na rawa tayi karfin halin cewa "In.. ina son hijab zan yi sallah" Maheer da duk jikinsa yayi sanyi ganin how uncomfortable she is just because he is close to her, cikin sanyin murya yace "Mimi yayanki ne fa" Sai a sannan ta daga ido ta kallesa for the first time.....
MAYRAAH is 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur Evidence via 07087865788 ki biya ki karanta hankalinki a kwance bbu hakki.
0 Comments